Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Sanarwar ƙasashen Amurka da Australiya da Japan ta saɓa wa doka

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan ne, ƙasashen Amurka da Australiya da Japan, sun fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa, inda suka gindaya sharaɗi game da aiwatar da “manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya”.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, wasu ƙasashe ƙalilan sun ƙara gindaya wasu sharuɗɗa, game da aiwatar da manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da zummar jirkita gaskiya, da ɓata wannan manufa, al’amarin da ya saɓa wa doka, wanda ƙasar Sin ta ki yarda da shi.

Rahotanni sun ce, ƙasashen Amurka, da Australiya, da Japan, sun fitar da wata sanarwar haɗin-gwiwa bayan da suka yi shawarwari, inda suka sake jaddada cewa, manufofinsu game da kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da matsayinsu kan batun Taiwan ba su canza ba, kana, sun kara wata jimla bayan “kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya” dake cewa, “a yanayin da ya dace”.

Bugu da ƙari, game da kalaman kakakin fadar White House dake Amurka, da suka shafi batun yankin Taiwan, Wang Wenbin ya ce, dalilan da ɓangaren Amurka ya fitar, ba za su iya ɓoye ainihin halin da ake ciki ba, wato Amurka ce take yunƙurin sauya halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, da ta’azzara halin da ake ciki, kuma Amurka ce take yunƙurin hura wutar rikici, kana Amurka ta gaza wajen sauke nauyin dake wuyanta.

Fassarawar Murtala Zhang