Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta aike da sammaci ga wasu jakadun ƙasashen turai da ƙungiyar EU don nuna rashin jin daɗinta

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin Deng Li ya aike da sammaci ga wasu jakadun ƙasashen Turai da ƙungiyar EU da ke ƙasar Sin, don nuna rashin jin daɗinta kan yadda ministan harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G7 da babban wakilin ƙungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da tsaro suka bayar da sanarwar nuna halin ko-in-kula kan batun yankin Taiwan na ƙasar Sin.

Deng ya bayyana cewa, sanarar da ministocin ƙasashen ƙungiyar G7 da kuma babban wakilin suka bayar, sun jirkita haƙiƙanin shaidu, wadanda suka mayar da fari baki.

Wannan tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan ƙasar Sin, da tsokanar siyasa. Wannan lamari tamkar aike mummunan sako ne ga ’yan a-waren yankin Taiwan. Don haka, ƙasar Sin ta nuna adawa da rashin jin daɗinta matuƙa.

Deng ya ƙara da cewa, manufar kasar Sin ɗaya tak a duniya, wata babbar ka’ida ce da ƙulla dangantaka a tsakanin ƙasa da ƙasa, wadda ta samu amincewar gammayar ƙasashen duniya. Haka kuma wannan manufa, ita ce tushen cuɗanyar Sin da sauran ƙasashe a siyasance, kuma babu wanda zai ƙalubalance ta.

Fassarawar Kande Gao