Ma’aikatar ilimi a Zamfara ta bankaɗo malamai 207 da ba su zuwa aiki

Daga SANUSI MUHAMMADa Gusau

Ma’aikatar ilimi, kimiya da fasaha ta Jihar Zamfara, tace binciken da ma’aikatar ta gudanar ya nuna cewa kimanin malamai 207 aka gano basu zuwa makarantun da aka tura su koyarwa, yanayin da ya jawo dakatar da albashin su na watanni uku.

Kwamishinan Ma’aikatar Malam Wadatau Madawaki ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Gusau yau Juma’a.

Kwamishinan ya kuma umarce su da su rubuta wasiƙar neman afuwa wadda za a miƙa wa gwamna Dauda Lawal domin domin ɗaukar mataki na gaba.

A cewarsa, ma’aikatar ta kafa wani kwamiti da ya yi aiki tuƙuru wajen bankaɗo matsalar ta rashin zuwa aiki a tsakanin malaman a shiyyar sanatoci uku dake jihar.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa bisa rahotanni da shawarwarin kwamitin, ya gano cewa malamai 207 ba sa zuwa aikin a makarantunsu musamman malaman sakandare.

Ya kuma koka da cewa rahotanni sun nuna cewa an gano wasu malaman suna karɓar albashi wuri biyu.

“Ma’aikatar bayan samun rahoton mun sanar da gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal da ma’aikatar kuɗi ta jihar, daga ƙarshe kuma gwamnatin ta bada shawarar a dakatar da albashin malaman da abin ya shafa.

“Gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar ta dakatar da albashin su har zuwa matakin ƙarshe da gwamnatin jihar za ta fitar kan lamarin”.

Ya kuma bayyana abin da malaman suke yi a matsayin rashin kishin ƙasa, yana mai cewa gwamnatin jihar da ma’aikatarsa ​​ba za ta lamunci duk wani aiki na sakaci da malaman jihar ke yi ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa malaman da abin ya shafa sun taru a ofishin kwamishinan inda suka amince da kuskuren da suka yi tare da miƙa takardar neman gafara a hukumance ga ma’aikatar.

Kazalika, kwamishinan bayan ya karɓi wasiƙun neman afuwar daga malaman da abin ya shafa da suka amsa laifinsu, ya yi alƙawarin kai wa gwamnan wasiƙun neman afuwar su domin ɗaukar matakin da ya dace.