Ma’aikatar jinƙai: An karkatar da N1.4bn tsakanin zamanin Sadiya da Edu – Bincike

Daga BASHIR ISAH

Sakamakon binciken Jaridar Premium Times ya nuna cewa, Ma’aikatar Jinƙai da Bunƙasa Walwala ta karkatar da kuɗaɗe sama da Naira biliyan 1.4 zuwa asusun wasu ma’aikata su takwas a ma’akatar a cikin sama da shekaru huɗu.

Bayanan da aka tattaro sun fallasa yadda aka yi ta hada-hadar kuɗi ta haramtacciyar hanya a ma’aikatar a zamanin shugabancin Sadiya Farouq da Betta Edu waɗanda a yanzu suke fuskantar bincike daga hukumar EFCC bisa zargin almundahana.

Idan za a iya tunawa, a lokutan baya-bayan nan ne Shugaban Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu bayan da ta ba da damar tura kuɗi Naira miliyan 583 zuwa wani asusu mai zaman kansa.

Tura kuɗaɗe har sau 118 da aka yi lokuta daban-daban  daga 2019 zuwa Disamban 2023, ya nuna abin damu ne ainun kan yadda ake facaka da kuɗaɗen ma’aikatar ba a bisa ƙa’ida ba.

Waɗanda aka tura wa kuɗaɗen kamar yadda sakamakon binciken ya nuna sun haɗa da Balogun Ibrahim da Ahmed Bomai da Oni Samuel da Adelana Kazeem da Oyegbile Adeniran da attahiru Zagga da Umar Idris, sai kuma Ezenekwe Chibuzor.

Bayanai sun ce abin a duba ne sannan a ɗauki matakin da ya dace kan yadda ma’aikatar ke dogaro da amfani asusun ɗaiɗaikun mutane wajen gudanar da hada-hadarta domin hana aukuwar hakan a gaba.