Daga BASHIR ISAH
Babban Ofishin Ma’aikatar Kuɗi na Ƙasa da ke Abuja, ya ƙaryata labarin da wasu kafofin yaɗa labarai suka yayata da safiyar Larab cewa gobara ta kama ofishin.
Taƙaitaccen bayanin da ma’aikatar kuɗin ta wallafa a shafinta na facebook da safen nan mai ɗauke da sa hannun mai bai wa Ministar Kuɗi shawara kan harkokin labarai da sadarwa, Yunusa Tanko Abdullahi, ya nuna abin da ya faru ba gobara ba ce, ɗan akasi ne aka samu a ma’ajin batura wanda kuma tuni an shawo kan matsalar ba tare da wani jinkiri ba.

Da safiyar nan wasu kafafen yaɗa labarai suka rawaito cewa an samu tashin gobara a babban ofishin ma’aikatar da ke Abuja.