Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babbar Lauyar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Beatrice Jeddy-Agba, ta bayyana cewa, Ma’aikatar Shari’ar ba ta samun wani kaso na kasafin kuɗi ba, don biyan basussukan shari’un da take gudanarwa ba.
Jeddy-Agba, wacce kuma ita ce babbar sakatariya a ma’aikatar ta shari’ar ƙasar, ta bayyana hakan a Abuja, Babban Birnin Tarayya, a wani taron tattaunawa kan samun hanyoyin magance take haƙƙin bil’adama a Nijeriya.
Taron mai taken ”Tattauna dabarun samun hanyoyin magance take haqqin bil’adama a Nijeriya” an shirya shi ne a bayan fagen taron ƙungiyar lauyoyin Nijeriya, NBA, da ke gudana a Abuja.
Jeddy-Agba, wadda Enoch Simon, darakta a sashin shari’a na ofishin babban mai shigar da ƙara na tarayya ya wakilta, ta ce, “Tun a shekarar 2019, ma’aikatar shari’a ta tarayya ba ta samu wani kaso na kasafin kuɗi ba domin biyan basussukan shari’a”.
Babbar Lauyar ta yi Allah-wadai da cewa, duk da tsarin doka da ake da su a ƙasar, gabatar da ƙararrakin da suka dace a kan lokaci tare da aiwatar da hukuncin da aka yanke, ya kasance babban ƙalubale ga gwamnati.
Ta ce, abin takaici ne yadda a ke yawan tilasta wa ma’aikatar biyan basussukan shari’a da ke fitowa daga ayyukan da hukumomi da jami’an tsaro suka yi ba bisa ƙa’ida ba.