Ma’aikatar Wajen Sin: Sin da EU sun cimma ra’ayi ɗaya kan fannoni da dama

Daga CMG HAUSA

Yau Asabar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta kira taron manema labarai, inda aka yi bayani kan ganawa karo na 23 a tsakanin shugabannin ƙasar Sin da ƙungiyar tarayyar ƙasashen Turai wato EU.

Shugaban hukumar kula da harkokin ƙasashen Turai na ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Wang Lutong, ya yi tsokaci yayin taron cewa, an sake shirya ganawar shugabannin Sin da EU ta shekara shekara, bayan shekaru biyu da suka gabata, ana iya cewa, ganawar ta kasance cuɗanya mafi muhimmanci a tsakanin shugabannin sassan biyu wato Sin da EU a bana, ta haifar da kyakkyawan sakamako, har ma sassan biyu sun cimma ra’ayi ɗaya a fannoni da dama.

Jami’in ya ƙara da cewa, ganawar ta nuna cewa, sassan biyu suna da aniyar yin ƙoƙari tare domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, tare kuma da sa kaimi kan farfaɗowar tattalin arzikin duniya.

Ban da haka kuma, sassan biyu wato Sin da EU su ma sun yi musanyar ra’ayi kan batutuwan ƙasa da ƙasa da suka jawo hankalinsu duka, misali rikicin ƙasar Ukraine, inda suka bayyana cewa, ya dace a daidaita rikicin ta hanyar tattaunawa.

Mai fassarawa: Jamila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *