Ma’auni biyu da Amurka da ƙasashen yammacin duniya suke amfani da su kan ‘yan gudun hijira yana nuna girman kai da son zuciyarsu

Daga CMG HAUSA

“A ƙasar Syria, duniya ta ga yadda aka riƙa kisan kiyashi da aka yiwa wata al’umma baki ɗaya, wanda ƙasashen yamma da dama suke da hannu a ciki, amma a ƙasar Ukraine, dukkan ƙasashen yammacin duniya na kare jama’arta.” Kwanan nan, jami’in kwamitin shawarwarin na Syria Anas Al-Abdah, ya bayyana yayin wata hira da ‘yan jarida cewa, bai ji irin “ma’aunai biyu” da ƙasashen yamma suke nunawa ba.

A jiya ne, ake cika shekaru 11 da tayar da rikicin ƙasar Syria. Amma ƙasashen yamma sun nuna matuƙar tausayawa ‘yan gudun hijirar na Ukraine, idan aka kwatanta da ƙoƙarin da suka yi na hana ‘yan gudun hijira daga wasu wurare, ciki har da Syria shiga ƙasashensu cikin ‘yan shekarun nan. Har ma wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labaru na ƙasashen yammacin Turai suna amfani da launin fata, ƙabilanci, da sauransu a matsayin ma’auni, inda suka fi martaba ‘yan gudun hijirar Ukraine fiye da na yankunan Gabas ta Tsakiya da na Afirka.

Kalaman da suka fallasa tsatsauran ra’ayi na ƙabilanci da kuma girman kansu na “Dora muhimmanci kan Turai da Amurka”. Suna ɗaukar ma’auni biyu kan ‘yan gudun hijira da aikin jin kai.

Kamar yadda wata ‘yar majalisar dokokin Turai Clare Daly ta ce, kawai suna ambatar Ukraine ne, amma ba a maganar Afganistan, domin Amurka ce ta mamaye Afghanistan.

Hakika Amurka ta taka mummunar rawa tun daga yakin Afganistan zuwa yakin Syria har da rikicin Ukraine. Kuma batun wanda aka damu da wanda ba a damu da shi ba, ba shi da alaka da adalci, gaba ɗaya ya samo asali ne sakamakon magudin haɗin gwiwa na ‘yan siyasar Amurka da kafofin yada labaran ƙasar. A ganinsu, ko ‘yan gudun hijira daga Gabas ta Tsakiya ko daga Ukraine, dukkansu wani makami ne kawai na neman cimma muradun siyasarsu da kuma nuna danniya ko babakere.

Fassarawa: Bilkisu