Mace mafi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118

Matar da ta fi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118 a birnin Toulon da ke yankin yammacin Faransa kamar yadda magajin garin ya sanar a hukumance.

An haifi Lucile Randon da ta kasance malamar majami’a a ranar 11 ga watan Fabairun shekarar 1904, wato bayan shekaru 10 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na farko, yayin da aka sanya ta a cikin jerin mutane mafiya tsufa a duniya a cikin watan Afrilun bara.

Bafaranshiyar ta yi aiki a matsayin malama mai koyarwa a gida a lokacin da take matashiya, wato gabanin ta mayar da hankali kacokan kan hidimar addini tana tsakan-kanin shekaru 40.

Gabanin mutuwarta, marigayiyar ta yi fama da larurar makanta, sannan ta ci gaba da rayuwa a kan kujerar marasa lafiya.

A shekarar 1944 ne, Randon ta sauya sunanta zuwa Sister Andre, yayin da kundin adana tarihi na duniya, Guiness Book of Record ya bayyana ta a matsayin ta biyu mafi tsufa a cikin al’ummar Faransawa da yankin Turai bakiɗaya da aka taba gani a duniya.