Maciji ya tilasta wa jirgin sama saukar gaggawa

An tilasta wa wani jirgin sama yin saukar gaggawa bayan wani ya ga maciji a cikin jirgin.

An hangi macijin a cikin gurbin fitilar da ta ke haska saman jirgin na Kamfanin AirAsia.

Jirgin ya taso ne daga Kuala Lumpur Babban Birnin Malaysia zuwa Gundumar Tawau da ke Jihar Sabah a Malesiya.

Har yanzu dai ba a bayyana wanda ya fara ganin macijin ba, amma an sanar da matuqan jirgin nan take, kuma Kyaftin ɗin jirgin ya yanke shawarar yin saukar gaggawa a birnin Kuching don yin feshin magani a jirgin da kuma cire macijin.

Wani fasinja ya wallafa bidiyon macijin a manhajar TikTok mai suna E-dal Tay (@edal8808), yana cewa, kalli yadda macijin ya ke tafiya a inda fasinjoji ke zaune a cikin jirgin sama.

Hoton bidiyon da aka wallafa mai ban tsoro ya samu kusan ra’ayoyin jama’a kusan miliyan uku da sharhi daga masu amfani da manhajar a duk faɗin duniya.

“Da gaske Maciji a cikin jirgin sama,” kamar yadda wani mai sharhi ya rubuta, yana kwatanta wani fim ɗin da aka yi a 2006 mai suna ‘Snake in the plane’.

“Sabon shafin tsoro ya buɗe ga fasinjoji,” Wani kuwa cewa ya yi, “wannan lamari ne mai ban tsoro kuma yana iya faruwa,” don hakan ya yarda da rahoton.

“Kamfanin Jiragen AirAsia na sane da lamarin da ya faru a jirgin da ya tashi daga Kuala Lumpur zuwa Tawau,” Babban jami’in tsaro na Kamfanin AirAsia, Liong Tien Ling, inda ya shaida wa tashar Labarai ta CNN ta Turkiyya lamarin.

Ya kuma qara da cewa, “an sanar da Kyaftin ɗin jirgin, nan take aka karkatar da jirgin zuwa birnin Kuching don yi masa feshin maganin da zai iya fitar da macijin.”

Ling ya kuma ce matuƙin jirgin ya ɗauki matakin da ya dace, ta hanyar ba da fifiko ga lafiyar fasinjoji da ma’aikatan jirgin ya kuma ambata cewa, bai san yadda maciji ya shiga cikin jirgin ba, inda ya bayyana faruwar hakan da abin mamaki.

“Wannan lamari ne da ba kasafai ya fiya faruwa a jirgin sama”.

Ling ya ƙara shaida wa Kafar Labarai ta Channel NewsAsia cewa, “Kyaftin ɗin ya ɗauki matakin da ya dace. Bai bata lokaci ko neman amincewar fasinjoji ko ma’aikatan jirgin da su ke ciki wajen sanya rayuwarsu a hatsari ba.”