Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya lashe babban zaɓen ƙasar da aka gudanar inda ya doke abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen.
Macron ya lashe zaɓen ƙasar ne wanda aka kammala a ranar Lahadi.
DW ta ruwaito cewa Mr. Macron ya samu kashi 58.2% cikin ɗari ne na ƙuri’un da aka kaɗa.
Yayin da abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen wadda ta amsa shan kaye, ta samu kashi 41.8% cikin ɗari.
‘Yar takarar adawar, Marine Le Pen, ta lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya musamman ma wajen ganin ta taka rawa a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da ke tafe.
Tuni ma shugabannin gwamnati da hukumomi da ma ‘yan siyasar nahiyar Turai suka taya Shugaba Macron murnar sake lashe zaɓen na Faransa.