Madarasatu Abdullahi Ibn Abbas ta yaye ɗalibai a Kaduna

Manhaja logo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ranar Lahadi ta makon jiya Makarantar Abdullahi Ibn Abbas ta gudanar da bikin yaye ɗalibanta a karon farko, wanda ya gudana a harabar makarantar da ke Unguwar Gangare, Yahaya Road by Kwanar Bishara, Rigasa Kaduna.

Taron, wanda ya samu halartar iyaye, ɗalibai, maƙwabta da sauran Jama’a, an gudanar da shi cikin tsari, wanda duk da karon farko ne, amma ya ba mutane sha’awa bisa irin kyakkyawan tsarin da aka gudanar.

Bikin, an gudanar da shi ne, inda yaye ɗalibai 34, waɗanda suka haɗa da mahaddata Alƙur’ani su 8, waɗanda kuma dukkansu mata ne. Sannan waɗanda suka sauke Alƙur’ani kuma su 26. Maza 6, mata 20.

Cikin jawabin da ya gabatar, Malam Ɗahiru Umar Hasan Arrigasiyyu, wanda kuma shi ne ya wakilci Shugaban Ƙaramar Hukumar Igabi, Hon. Jabir, ya yaba wa shugaban wannan makaranta ne bisa irin gudumawar da ya ke bayarwa wajen ci gaban ilimi da tarbiyya a wannan yanki na Rigasa.

Daga nan sai Malamin ya bayyana cewa Hon. Jabir ya ce a nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda ake samun taɓarɓarewar tarbiyya ga matasa, wanda ya ce wasu kafafen yaɗa labarai na talbijin suke taimakawa wajen vatawa.

Hon. Jabir ya ce za ka ga Malamai da iyaye sun dage wajen bayar da tarbiyya, amma muddun aka bar yara suna kallon shirye-shiryen da ake yi a waɗannan gidajen talbijin, to tarbiyya na rushewa cikin ƙanƙanin lokaci.

Don haka ya yi kira ga iyaye su kasance masu sanya ido wajen tsawatarwa bisa kalle-kallen da yaran su ke yi. “Bai kamata iyaye su sake wasu kafafen yaɗa labarai suna vata ma ‘ya’yan su tarbiyyar da ake ba su a makarantu da gidaje ba,” inji shi.

Haka kuma Shugaban na Ƙaramar Hukumar Igabi ya nuna takaicin sa bisa yadda shaye-shaye suka yi yawa tsakanin maza da mata.

Yana mai cewa “yanzu wannan bala’i ya yawaita hatta a cikin matan aure. Za ka ga mace ta sanya hijabi ta saɓa jaka tana bi guda-gida, alhali babu komai a cikin jakar nan sai ƙwayoyi da sauran kayan shaye-shaye. “

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu ƙwaya ta ɓata matasan mu maza ta mata. Don haka wajibin mu ne kowa ya bayar da gudamawarsa wajen magance wannan matsala.

Da ya ke zantawa da manema labarai a harabar wannan makaranta, Shugaban ta, Imam Ibrahim Adam Imam ya bayyana cewa an buɗe wannan makaranta ce a shekarar 2018 da ɗalibai 12, amma cikin ikon Allah ga shi yau har sun yaye ɗalibai 34.

Imam Malam Ibrahim ya ci gaba da bayyana wa manema labaran cewa yanzu haka suna da cikakkiyar rajista da Hukuamar kula da makarantun Islamiyya, sannan sun kammala duk shirye-shiryen da suka wajaba wajen yin rajista da Hukumar yi wa kamfanoni rajista ta ƙasa, CAC.

Game da matsalolin da makarantar ke fuskanta kuwa, Malam Ibrahim cewa ya yi, kamar yadda kowane abu ke da matsalolin sa, su kuma babbar matsalar su ita ce ta rashin biyan kuɗin makaranta da iyaye ba sa son yi, wanda ya ce wanan ba ƙaramin cikas ya ke kawo masu ba.

Daga nan sai ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da suna biyan kuɗin karatun ‘ya’yansu a kan lokaci, domin da waɗannan kuɗaɗe ne ake samun abin da ake biyan Malaman da suke koyarwa.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, ɗaya daga cikin waɗanda ‘ya’yan su suka sauka a wannan rana, wanda ɗaya ta haddace Alƙur’ani, ɗaya kuma ta yi sauka, wato Malam Idris Abdussalam, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa da godiya ga Allah da ya nuna masu wannan rana, wacce ya ce rana ce mai cike da tarihi a rayuwarsa.

Malam Idris ya ci gaba da da bayyana cewa wannan ne karo na farko da ya taɓa samun wanda ya haddace Alƙur’ani a gidansa. Don haka yana godiya ga Allah bisa wannan ni’ima.

Ita dai wannan makaranta tana ɗauke da sashen boko da kuma Islamiyya. Haka kuma shi Shugaban wannan makaranta, akwai wasu ɗalibai masu yawa, waɗanda yawancinsu marayu ne da kuma mara ƙarfi, waɗanda suke karatu a wannan makaranta kyauta, duk ya ɗauke masu ɗawainiyar karatun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *