Madarasatul Irshad Littahfizul Ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 30 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas

Makarantar Madarsatul Irshad Litfahfizul  Ƙur’an dake lamba 9, kan titin Olowolagba a babbar kasuwar ƙasa da ƙasa wadda aka fi sani da suna kasuwar Mile1 da ke Legas ta yaye ɗalibai yara maza da mata sama da talatin.

Taron ya gudana ne a harabar makarantar firamari dake kan titin Maidan a ranar Lahadin ƙarshen makon jiya.

 Babban sakataren kasuwar ta Mile 12, Alhaji Idiris Balarabe Kano shi ne ya wakilci babban shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Dallatun Egbaland Abeokuta) a wajen taron kuma shi ya jagoranci shuwagabannin ɓangarorin kasuwar a wajan taron.

Tunda farko dai bayan buɗe taro da addu’a ne aka kira Zainab Usman ‘yar gidan shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman da sauran ɗaliban da makarantar ta yaye ɗaya bayan ɗaya suka karanto kaɗan daga cikin ayoyin Alƙur’ani mai tsarki, inda daga bisa kuma aka buɗe gidauniyar neman taimakon ci gaba da gudanar da ayyukan makarantar.

Alhaji Shehu ya ce wannan shine karo na ukku da makarantar ta yi taron yaye ɗaliban, ya ce wanda suma suna can sun samu aiki a waɗansu wurare, ya ce waɗansu kuma sun samu aiki a cikin makarantar suna koyar da sababbin ɗaliban makarantar.

Ya cigaba da jinjina wa malamai da sauran ‘yan kwamitin makarantar, a ƙoƙarin su na bai wa yara ilimin addinin Musulunci. Bugu da qari babban sakataren kasuwar ta Mile12 ya ci gaba da jinjina wa shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman bisa ga gudunmawar da ya ke bai wa makarantun Islamiyoyi a unguwar domin faɗaɗa karatun addinin Musulunci.

Ya kuma taya yara ɗaliban murna musamman ɗaliban da makarantar ta yaye a wannan lokaci tare da ba su shawara da su duƙufa a wajen cigaba da neman ilimin addinin Musulunci dama na zamani bakiɗaya.