Madubi: Namiji shi ne makarantar matarsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafin ma’aurata na zamantakewa. A wannan mako mun zo da jawabi a kan yadda mata suke canzawa bayan aure. Kamar yadda wani makarancin wannan filin ya yi min ƙorafin cewa, wai me ya sa ba za a ja kunnen a kan mata su daina canzawa bayan aure ba?

Domin a cewar sa, mace tana canzawa daga yadda aka aure ta. Wato ta sauya daga yarinyar kirki mai hankali da biyayya da sanin ya kamata, zuwa mara kunya, mara kulawa, mara biyayya, da sauransu dai. Ba kamar dai yadda take lokacin kafin aurenku ko kuma farkon zaman aurenku. Tabbas hakan na iya faruwa. Kuma bayan faruwar, namiji kan rasa gane kai da ƙafar matarsa.

Sai dai kuma da farko zan fara shimfiɗa a kan wannan al’amarin. Ya kamata maza su sani akwai dalilai na sauyi na rayuwa akwai kuma wanda ita matar matsalarsa take jawowa, sannan akwai kuma kaso mafi yawa wanda kai ne kake jawowa.

Da farko, sauyi na rayuwa da ma Hausawa sun ce, yau da gobe tana sa a mari Amarya. Sannan kuma, ‘yau da gobe, ta ƙi wasa’. To wannan lamari yana sa lokaci zai sa soyayyar ta ɗan sane. Musamman ma auren da aka gina a kan sha’awa.

Daga namiji ya biya buƙatarsa sai ya ji ma duk zaman ya gundure shi. Haka ita ma matar idan kallon kuɗi take masa za ta ji duk ya gundure ta, sai a koma zaman haƙuri. Abin lura shi ne, tunda ba wannan soyayyar ta farko kafin aure dole sai dai a ji tsoron Allah kuma a riƙe amanar juna.

Haka abin dubawa shi ne, kafin aure suna ta ɗokin juna ne, ba wanda ya san ya wane yake. Amma da zarar an yi aure kowa ya san makwantar juna, ya kwana gabanta, ya tashi gabanta duk wani yanayi nasa ta gani ta sani, sai wata mace ta dinga ganin namiji a raine tana ganin to barazanar me zai yi masa ta san shi a ɗa namiji ta san komai?

Wannan yana sa mata su canza sosai. Yau da gobe in dai kana tare da mutum sai an ɗan yi wannan raunin. Da ma an tambayi ido wa ka raina? Sai ya ce: “wanda nake gani kullum”!

Dalili na biyu kuma, akwai dalili daga matar. Wasu mata suna da dogon buri su auri mai maiqo. Wannan yana sa maza su yi musu ƙarya idan ta shigo ta ga da ma ba haka ba ne, sai ta canza daga yarinyar kirki ta fara wulaƙanci iri-iri.

Ko kuma yadda ya saba mata hidima a baya ya ɗan janye saboda hidimar iyali yanzu ta hau kansa. Ko kuma arzikin ne ya ja baya, ba yadda Allah bai iya ba. Wata kuma da ma tana auren ne na hana rantsuwa, kar dai a ce ba ta yi auren ba.

Za ta yi ta kwantar da kai ga namiji kafin ta shigo. Tana shigowa, shikenan wa Allah ya haɗa ta da shi kuma? Sai tijara kala-kala don ya gaji ya sake ta. Wata kuma ba sakin take so ba, kawai tijara ce sai ta yi.

Wataƙila tana ganin ba shi da kuɗin auren wata matar ne, dole ya zauna da ita. Sannan zuga ma daga dangi ko ƙawayen matar yana matuƙar taka rawa a nan. Dukkan waɗannan dalilai laifin matar ne.

Sai dalili na uku ta ɓangaren ka kai namiji wanda kake jawowa. Domin kamar yadda taken ya nuna, kai namiji kai ne makarantar matarka. Idan an ce makaranta kuwa, ana nufin inda ake koyo. Ashe kenan kai ne Malaminta, a wajenka take koyon dukkan wata ɗabi’a ta zaman aure da yadda za ta girmama ka ko akasin haka.

Dukkanninmu shaida ne dai a farkon aure mace tana da matuƙar yadda da kuma girmama namiji. A farko tana ɗaukarsu kamar mahaifanta, sai daga baya idonta ya buɗe ta fara sauya hali.

Abin tambayar me yake sauya mata halayen? Bayan waɗancan ɗabi’u da na lasafta a baya, akwai wasu dalilan kuma da suka dogara kacokan ga namiji.

Waɗannan dalilai sun haɗa da:

  • Na farko akwai ƙarya. Mace kan ba wa miji dukkan yarda kafin da kuma a farkon aure su. Kuma kada a manta da akwai manufofi da suke ta ɗawainiya da ita. Sannan akwai imani tun na filazal cewa namiji ba ɗan goyon ba ne da sauransu.

Wata ma ta ɗanɗana kuɗarta wajen wasu mazan. Banda wanda ta gani a danginsu da ƙawaye da sauransu. To duk da dai wannan imanin ya zama ruwan dare, ba kowacce mace ce take yarda da shi, ɗari bisa ɗari ba har sai ya faru a kanta. To mace kan zo da wannan imanin amma ba ta gama gaskata shi ba sosai. Kawai dakonka take ka kuskure.

To daga lokacin da ka yi mata qarya ko yaya, ko ka yi yunƙurin cin amanar ta, sai ta ji ai kawai ta gaskata karatun waɗancan yanuwan nata mata a kan namiji. Sai kuma ita ma ta daina amincewa da dukkan abubuwan da ka faɗa. Kamar yadda wasu maza kan yi wa mace ƙarya ta arziki a waje, da an yi aure, sai ka ga ta ga ba haka ba ne. Ka ga ka koya mata ta raina ka kada ta ga girmanka.

Don haka, maza a dinga gaskiya da gaskiya. Ba sai ka yi ƙarya ba, in dai matarka ce, za ka aure ta. Idan ba ka same ta ba kuma, to ba rabonka. Haka a gidan aure duk da akwai sanda ƙarya take halasta ko ta zama lalura ko ma dole, a yi abin cikin hikima. Mace ba ta da aljanna ko wuta. A faɗa mata gaskiyar da za ta ɗauka. A rage yaudara da ƙarya.

*Rashin tsaya mata a danginka ko wani da yake cin mutuncinta. Mace idan namiji yana mata haka, shi ma yana sa ya fita a ranta. Ta fita sabgarsa. A fili dai za a ɗan yi shiri. Amma a zuciyarsa sam ba ta ganin darajar ka. Kuma kai ka jawo.

*Son kai: Namiji ma yana koyar da abokiyar zamansa son kai ta hanyar fifita kansa ko ‘ya’yansa ko danginsa bisanta. An san kowa yana da nasa muhimmancin. Amma matarka ma na da nata muhimmancin na musamman domin tana yi maka abinda ba wanda yake maka shi.

Ƙasƙantar da ita a kan wasu yana sa ita ma ta ji ka fita a ranta ta fara koyon yadda za ta samu wannan ƙima. Wajen ƙawaye, ‘yanuwa da sauransu. Ka koya mata ta daina dogaro da kai don samun farin cikinta. Ta nema a wani waje.

*Wulaƙantata da zaginta: Wannan yana koya wa mace ta tsane ka, tsana mai tsanani da za ta sa ta dinga fatan duk wani mugun abu ma ya same ka. Irin wannan har addu’a mummunan suna iya yi wa maza. Ko kuma a hankali yayin da ka zo kana cin mutuncinta tana shiru, wata har koyon mayar maka da magana za ta yi. Wata ma sai ta ɗaga sautinta fiye da nasa, wanda haramun ne. Allah ya kiyashe mu.

*Cuzguna mata ta hanyar horar da ita da hana ta zuwa unguwa, ko ƙin cin abinci ta da sauransu, shi kuma wannan kana koyar da ita taurin kai ne. Ta dinga ganin to idan ma ka yi sai me? Ita ma tun tana haƙuri har ta fara nemo hanyoyin da za ta dinga cuzguna maka cikin sauqi. Domin ta samu ta huce daga irin abinda kake yi mata.

*Rowa da voye-voyen sirri: Namiji mai rowa da ɓoye-ɓoyen sirri yana koya wa matarsa ita ma ta dinga haka. Kuma ta daina jin tausayinka.

*Rance da rashin sauke nauyi: Yawan karɓar kuɗin mace a cinye da kuma rashin sauke nauyin iyali yana sa mace ta koyi yi wa namiji ɓoye-ɓoyen aya kuɗin saboda tana tsoron ka ranta ka ƙi biya.

*Rashin adalci tsakanin mata ma yana sa mace ta zare jikinta gabaɗaya da zuciyarta daga gare ka. Wasu maza na gane hakan, wasu kuma ba lallai su gane ba. Ga ka tare da mace amma ta yi nisan kiwo a zuciya. Ta daina shauƙin yin abu don faranta maka, kuma ba za ta ji tausayinka ba. Saboda ita ma tana ganin kamar ba ka tausaya mata.

Hakazalika, rashin sauraren ta da jin damuwarta zai sa ta nemo wani abokin shawarar wanda za ta kashe su binne. Kai kuma ta ɗauke maka wuta ta daina ma tunkararka da duk wani abu da ya shafe ta.

Haka rashin ɗaukar lamurran ta da muhimmanci ma yana sa ita ma daina ɗaukar naka da muhimmanci. Misali, idan ba ka girmama mata iyaye da dangi, ita ma fa watarana za a wayi gari ta daina ƙimantaka da dukkan ma wanda ya shafe ka.

Don haka, kawai abinda ya kamata namiji ya zama babban ƙawar matarsa. Su fahimci juna, a gudu tare, a tsira tare. Don zaman aure ba barikin soja ba ne. Ka sakar mata jiki, amma kada ka yarda ko da wasa ta raina ka. Raini yana sa namiji gabaɗaya ya kasa jin daɗin zama da matarsa.

Don haka, a gyara hali a duba abinda Allah ya ce na amana da aka ba ku mata. Ba baiwa ko wulaƙantaciya ba ce. Duk abinda za ka yi mata ka yi mata da tausayi da jin ƙai kamar yadda kakar so wani namijin ya yi wa ‘yarka mace ko ‘yaruwarka.

Su kuma mata, su ji tsoron Allah, su san aure neman aljanna ne. Karin maganar Bahaushe na cewa, “wanda ya yi maka kan kara, ka yi masa na ice” banda gidan aure ake nufi. Allah ya ce ki bishi ba wai duk abinda ya yi ko ce sai kin rama ba ko sai ya yi miki tasiri ba.

Biyayya Allah ya umarce ki ki yi. Idan ya zalunce ki, shi Allah zai hukunta shi, ke kin fita haƙƙinsa. Amma hakan da wahala sai an daure. Allah ya datar da mu. Sai wani makon idan rai ya kai.