Mafi ƙarancin albashi: Yayin da ake ƙarƙare batun a ranar Litinin, gwamnati ta gabatar da naira 62,000 ga NLC da masu ruwa da tsaki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A yau Litinin ne ake sa ran kammala batun ƙayyade mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Najeriya, yayin da ƙungiyoyin ƙwado ke sauraron amsar tayin naira 250,000 daga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta yi.

Shuwagabannin ƙungiyoyin ƙwado na ƙasa sun bada wa’adin 10 ga watan yuni a matsayin ranar ƙarshe da zasu saurari amsar gwamnatin tarayya game da batun.

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne kwamitin ƙayyade ƙarancin albashi ta ƙasa ta gudanar da wani zama, inda aka cimma yarjejeniyar naira dubu 62 tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da kuma na haɗaɗɗiyar kungiyar ma’aikatu masu zaman kansu, sai dai NLC ta ce tana kan bakanta na naira dubu 250.

Akasin haka ne kuma, wata sanarwa da aka fitar daga ɓangaren gwamnoni ta ce naira dubu 57 ne abun da zasu iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a jihohinsu.

Rahoto daga jaridar ‘News Point Nigeria’ yayi nuni da cewa, shuwagabannin ƙungiyoyin ƙwado a mataki na ƙasa ka iya yanke shawarar shiga yajin aiki la’akari da sakamakon amsar gwamnatin tarayya kan batun.

A makon da ya gabata ne, ƙungiyoyin ƙwado suka zartar da yajin aikin gargadi na kwana biyu kan batun ƙarancin albashi da kuma hauhawar farashin wutar lantarki a fadin Najeriya wanda aka janye bayan wani zama tsakanin wakilan ƙungiyoyin da kuma na majalisar tarayya.