Magu ya miƙa takardar neman murabus

Daga BASHIR ISAH

Tsohon shugaban riƙo na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗi (EFCC) Ibrahim Magu, ya miƙa takardar neman yin murabus ga hukumomin da suka dace don su shirya murabus ɗin nasa kamar dai yadda jaridar Daily Nigerian ta kalato.

An haifi Magu ne ran 5 ga Mayun 1962, wanda bisa lassafi ya kamata ya yi murabus daga aiki a ranar 5 ga Mayun 2022 bayan da ya cika shekara 60 da haihuwa.

Magu ya shiga aikin ɗan sanda ne a ranar 3 ga Maris, 1990 a matsayin ASP inda ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Afrilun 2018.

Tun bayan badaƙalar tsare shi da aka yi a watan Yulin 2020, babu wani sauyin wajen aiki da aka yi ma Magu.

Hukumar Kula da Harkokin ‘yan Sanda (PSC) ta dakatar da yunƙurin yi wa Magu ƙarin girma zuwa matsayin Mataimakin Sufeto Janar (AIG), har sai ta samu amincewar ofishin Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a da kuma ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.

Tun a ranar 20 ga Nuwamban 2020 aka miƙa wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari rahoton binciken da kwamitin Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Ayo Salami ya gudanar kan badaƙalar Magu amma har yanzu ba a bayyana wa jama’a abin da rahoton ya ƙunsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *