Mahaƙar ɗanyen mai ta Daqing ta samar da tan biliyan 2.4

Daga CMG HAUSA

Sashen dake lura da mahakar mai ta Daqing, dake ƙarƙashin babban kamfanin albarkatun man fetur na ƙasar Sin, ya ce kawo yanzu, mahakar ɗanyen mai ta Daqing, ta samar da jimillar ɗanyen mai da yawan sa ya kai sama da tan biliyan 2.4, tun fara aikin ta a shekarar 1959.

Mahakar man dai na kan gaba, wajen samar da albarkatun mai a ƙasar Sin, ta kuma samar da kaso 40 bisa ɗari, na ɗaukacin albarkatun man da ake hakowa a ƙasar Sin a tsawon wannan lokaci.

Cikin shekaru sama da 60, mahakar Daqing ta gudanar da aiki ba tsayawa, inda ta taba jera shekaru 27, tana samar da ɗanyen mai da yawan sa ya kai sama da tan miliyan 50 a ko wace shekara.

A kuma shekarun baya-bayan nan, adadin mai da iskar gas da take samarwa ya haura kimanin tan miliyan 40 duk shekara.

Mahakar Daqing dai na cikin manyan cibiyoyin hako mai a ƙasar Sin, tana kuma yankin lardin Heilongjiang, dake Arewa maso gabashin ƙasar Sin.

Ta kuma ba da gagarumar gudummawa ga zamanintar da masana’antar sarrafa albarkatun man fetur a ƙasar Sin.

Mai fassara: Saminu Alhassan