Mahaifinka ka ke zuɓar wa da ƙima a Arewa – Adnan ga Seyi Tinubu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a zaɓen 2019, Kwamared Adnan Mukhtar Tudun-Wada ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya daina yiwa mahaifinsa talla a Arewa.

Adnan wanda ya ƙware a fannin hulɗa da jama’a kuma malami a jami’a, ya bayyana ziyarar buɗa baki da ɗan shugaban ƙasa ke yi a kwanakin nan tare da raba shinkafa a matsayin cin mutunci ga Arewa.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja.

Mukhtar wanda kuma ya nemi zama ɗan majalisar dokokin Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) yayi kira ga Seyi Tinubu da ya daina rangadin buɗa baki a Arewa ta hanyar mayar da hankali kan wani abu da zai kyautata rayuwar matasa a yankin, wanda shi ya kamata gwamnati ta bada ba fifiko ba siyasa ba.

“A matsayina na matashi ina so in gaya wa ɗan Shugaban ƙasa cewa wannan ba lokacin yaƙin neman zaɓe ba ne, lokacin mulki ne shekara biyu ya rage a yi zaɓen 2027″.

‘’Saboda bai mutunta Arewa ba, shi ya sa yake raba mana shinkafa kamar mabarata. Wannan ba abin da muke buƙata ba ne, Shugaban Ƙasa ya fito da ƙudirin gyara haraji don kawo cikas ga Arewa, hanyar Abuja zuwa Kano ba a kammala ba, masana’antunmu ba su yin aiki, Katsina, Zamfara da wasu sassan Sakkwato ba su da tsaro,” inji sanarwar.

Ya kamata ya sanar da mahaifinsa cewa Arewa na kukan wariya. An mayar da mu gefe. A bar shugaban ƙasa ya magance mana matsalolinmu, amma zuwa Arewa a ba mu abinci cin mutunci ne.

‘’Ko zai iya yin abubuwa irin haka a kudu, Legas musamman inda ya fito? ”

‘’Duba yadda yake zaune a fadar sarakunan gargajiyar mu, ba tare da girmamawa ba”.

‘’ Yadda ya yi hannu da Sarkin Zazzau ba tare da girmama al’adunmu ba. Shin zai iya yi da Oba na Legas ko Oni na Ife haka?

‘’Ina kira ga duk wani matashi mai kishi da ya fito ya nisanta kansa daga ayyukan Seyi Tinubu, wanda ba a zaɓe shi ba kuma ba ya riƙe da muƙamin siyasa a gwamnatin mahaifinsa kai ka taɓa ganin ƴar Donald Trump ko Barack Obama suna haka?” Inji Adnan