Aminu Ala ya yi babban rashi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Allah Ya yi wa Hajiya Bilkisu Sharif Adam, mahaifiyar shahararren mawaƙin Hausa Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa) rasuwa.

Marigayiyar ta rasu tana da shekara 70 a duniya, ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu, Aminu Ladan Abubakar da kuma ‘yar’uwarsa Khadija.

Da safiyar wannan Talatar misalin ƙarfe 9 ake sa ran gudanar da jana’izar ta a gidansa da ke Maidile a birnin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *