Mahaifiyar Mawaƙi Wizkid ta zama riga mu gidan gaskiya

Daga AISHA ASAS 

Shahararren mawaƙin da tauraruwarsa ke haskawa a wannan zamani, Ayodeji Ibrahim Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya yi babban rashi, inda mutuwa ta ɗauke mahaifiyarsa mai suna Misis Jane Dolapo.

An ruwaito cewa, Misis Balogun ta mutu ne a ranar Juma’a, sai dai har zuwa yanzu babu wani cikakken bayanin abinda ya yi sanadin ajalinta. Sannan ba a ji komai daga bakin ɗan nata mawaƙi Wizkid ba.

Watakila hakan ba ya rasa nasaba da zamewarta ginshiƙi ga rayuwarsa, domin ta ba shi goyon baya, kuma ta kasance ƙwarin gwiwa gare shi akan harkar waƙan da yake yi. 

Mai karatu zai amince ne idan ya yi waiwaye ga yadda aka sha haskota a wuraren gasar waƙoƙi da kuma bukuwan da ɗan nata yake zuwa, tana ba shi ƙwarin gwiwa ta hanyar nuna abinda yake ya yi, kuma tana tare da shi.

Wannan kawai zai tabbata da cewa, ba kawai tana zuwa inda ɗan nata ke wasa ba don jin daɗin waƙoƙinsa ba, sai don ta nuna masa tana tare da shi a duniyar da yake ciki ta waƙoƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *