Mahalarta taron dandalin Boao sun yi kira ga ƙasa da ƙasa da su ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da cutar Covid-19

Daga CMG HAUSA

Har zuwa yanzu, cutar Covid-19 na ɗaya daga cikin ƙalubalolin da ’yan Adam ke fuskanta. A gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao da ke gudana, mahalarta taron sun ba da shawarwarinsu ta fannin rage giɓin da ke tsakanin ƙasa da ƙasa ta fannin yaƙi da cutar, waɗanda kuma suka yi nuni da cewa, ƙasar Sin na ba da babbar gudummawa ta wannan fanni.

Alƙaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, bayan da ƙasar Sin ta ƙirƙiro rigakafin cutar, ya zuwa yanzu ta riga ta samar da alluran rigakafin sama da biliyan 2.1 ga ƙasashe da ƙungiyoyin duniya sama da 120, kuma ta raba fasahohinta ga ƙasashe sama da 20. Baƙi mahalarta taron sun amince da ƙoƙarin da ƙasar Sin take yi, ta fannin rage giɓin da ke tsakanin ƙasa da ƙasa ta fannin shawo kan cutar.

Gargee Ghosh, babbar jami’ar kula da gidauniyar Bill & Melinda Gates, ta bayyana cewa, “Sakamakon ƙirƙire-ƙirƙiren da ake ta yi a kasar, da ma ƙaruwar ƙarfinta na samar da kayayyaki, da kuma ƙaruwar alkawuran da aka ɗauka na haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, ƙasar Sin ta riga ta zamanto ƙasar da ke taka muhimmiyar rawa, wajen rage giɓin dake tsakanin ƙasa da ƙasa a ɓangaren shawo kan cutar Covid-19.”

A nasa jawabi, mataimakin shugaban hukumar raya haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa ta ƙasar Sin, Mr. Deng Boqing ya ce, yawan rigakafin da ƙasar Sin ke iya samarwa a ƙetare ya kai biliyan ɗaya a shekara, kuma ƙasar Sin tana son ƙara inganta haɗin gwiwa da kasa da kasa, don ba da gudummawarta wajen sauƙaƙa gibin da ke tsakanin ƙasa da ƙasa ta fannin shawo kan cutar Covid-19.”

Fassarawa: Lubabatu