Mahara sun kashe mutane kimanin 10 a Ƙaramar Hukumar Batsari

Daga BABANGIDA GORA a Katsina

Kimanin mahara sama da ɗari ne su kai dirar mikiya a wata unguwa da ke cikin garin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Maharan da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne, da su kai ƙaurin suna a yankin na Batsari da ke makwabtaka da jihar Zamfara da ta daɗe tana fama da  masu garkuwa da mutane da satar shanu tsawon lokuta, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Haka zalika maharan sun kai wannan farmaki ne a ranar Talatar da ta gabata da misalin ƙarfe 8:00 na dare, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da goma.

Rahotanni sun yi nuni da cewa `yan bindigar sun qona wasu motoci da babura a lokacin da suke kai harin a cikin unguwar.

Haka kuma a lokacin da wakilin mu ya tuntuɓi rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da faruwar wannan lamari tare da ƙara ƙaimin ganin an ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen lamarin.