Mahawarar masana shari’a kan cancantar takarar Goodluck Jonathan a 2023

Daga JOHN WADA, LAFIYA

A ’yan kwanakin nan ne al’ummar Nijeriya suka yi ta ji suna kuma karanta wata muhawara ta musamman tsakanin sanannu kuma  ƙwararrun nan biyu a fannin shari’a wato, Femi Falana (SAN) da Mike Ozekhome (SAN). Ana tafka muhawarar ne a kan ko tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya cancanci sake fitowa takarar kujerar ta shugaban ƙasa a karon nan, ko bai cancanta ba. A wannan rahoto na musamman, wakilinmu John D. Wada ya yi nazari a kan mahawarar tasu da matsayar su ga niyyar takarar Jonathan ɗin kamar haka:

A yayin da zaɓukan shekarar 2023 ke cigaba da gabatowa, wasu sanannu kuma ƙwararrun  a fannin shari’a su biyu wato Femi Falana (SAN) da Mike Ozekhome (SAN) suna cigaba da tafka wata muhawara ta musamman a kan ko a dokan e ya dace tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a 2023 ko bai dace ba? Sakamakon rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’adua sai Goodluck Jonathan a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa ya karɓi ragamar mulki don kammala sauran wa’adin Yar’adua da ya rage. Kundin tsarin mulkin ƙasar nan dai na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska ya bayyana cewa, duk shugaban ƙasar da aka zaɓa zai yi shekaru 4 ne daga ranar da ya ɗauki rantsuwar kama aiki. Kamar yadda shashi na 137 na kundin tsarin mulkin ya tanadar.

Hakan na nufin mutun bai cancanci sake fitowa takara ba ko kuma a zaɓe shi a kujerar shugaban ƙasa ba muddin an riga an zaɓe shi sau 2 a baya. Sai dai abinda ya kasance muhawara tsakanin ƙwararrun lauyoyin biyu shi ne, ko rantsar da Goodluck Jonathan na farko da aka yi a 2010 yana matsayin wa’adinsa na farko kenan, idan aka yi la’akari da tanadin dokar ta sashe na 137. Hakan na kuma nufin bayan wanda aka sake masa a 2011, shikenan ba shi da damar sake fitowa takarar? Maƙasudin muhawarar kenan.

Femi Falana  (SAN):
A nasa ɓangaren, wannan ƙwararren lauya dake fafutukar kare haƙƙin ‘yan adam, Femi Falana, kuma wanda shi ya fara ta da mahawarar bayan ya sanar a hukumance kimanin makwanni biyu da suka gabata cewa, bayan an rantsar da Jonathan sau biyu a matsayin shugaban ƙasa don haka, a yanzu bai cancanci sake fitowa takarar ba. Femi Falana ya kafe, ya kuma jaddada cewa, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan bai cancanci fitowa takarar ba. Falana ya fake da tanade-tanaden waccan dokar a matsayin hujjojinsa. A cewar sa, Jonathan wanda ya kasance shugaban ƙasar Najeriya tsakanin shekarun 2010 da 2015. Don haka yake ganin zai karya dokar shekaru 8 wato wa’adi biyu kenan da aka keɓe wa kowanne shugaban ƙasa, idan har ya sake fitowa takara a 2023, ya kuma yi nasara.

Ya cigaba da bayyana cewa, “Dakta Goodluck Jonathan bai cancanci sake fitowa takarar kujerar shugaban ƙasa a 2023 dake tafe ba. Dalilin kuwa shi ne, idan ya fito ya kuma lashe zaɓen, zai sake yi ƙarin shekaru 4 kenan. Hakan na nufin zai yi shekaru 12 kenan a matsayin shugaban ƙasar Najeriya. Hakan ba shakka ya karya tanadin dokar mulkin ƙasar nan na sashi 137 wanda ya tanadar da shekaru 8 ne kawai.” Inji Falana. Babban lauyan ya kuma bayyana cewa, idan aka yi la’akari da tanadin sashi 137 na dokar, Jonatah ba zai iya sake neman kujerar ba bayan ya kammala wa’adin marigayi Umaru Musa Yar’adua, aka kuma sake rantsar da shi na cikakken wa’adin shekaru 4 a 2011 bayan ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a sunansa (Goodluck Jonathan). Ya ce, “Mutumin da aka rantsar da shi ya kammala wa’adin wani da aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa ba za a sake zaɓensa a kujerar sama da shekaru 4 a gaba ba, kamar yadda shi kuma sashe na 137 na sashe (3) ya tanadar kenan.

Femi Falana ya ƙara da cewa, majalisar dattawa ta tarayya rukuni na 4 ne suka ƙirƙiro da dokar, yayin da shi kuma shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu, ta zama doka a watar Yunin shekarar 2018. Ya kuma ƙalubalanci batun cewa dokar ta 2018 bata shafi Jonathan ba kasancewar ya bar kujerar bayan ya faɗi zaɓen 2015 wanda Shugaba Buhari ya lashe. Har’ila yau, Femi Falana ya ba da misali yadda tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja ya kasa samun damar ƙarin wa’adinsa don maye gurbin lokaci da ya yi a waje, bayan majalisar dokokin jihar ta tsige shi ba bisa ƙa’ida ba. A cewar sa, kotun koli ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan na ƙarin wa’adin tana mai bayyana cewa, kowanne gwamna yana da damar yin wa’adin shekaru 8 ne kacal ko ƙasa da haka, ba sama da haka ba.

Mike Ozekhome (SAN):
Shi kuma a nasa ɓangaren babban lauyan na biyu wato, Mike Ozekhome (SAN) ya bayyana rashin amincewarsa da hujjojin da Femi Falana ya gabatar. Inda shi kuma Mike Ozekhome yake cewa sabuwar dokar ba ta shafi Jonathan ba.

Ya ce, “Sanin kowanne lauya ne cewa dokokinmu na ƙasar nan kamar na wasu ƙasashen waje da dama sun haramta yin amfani da sabuwar doka ta yau a kan batuttuwa da suka gabata. Shi ya sa dokar sashe na 4 na tanadin kundin tsarin mulki ya yi bayyani kamar haka “Majalisar dattawa ko ta dokokin jihohin ƙasar nan bakiɗaya basu da wata dama ko ikon kafa wata doka da ka iya shafar batuttuwan baya da na yanzu.” Wannan sabuwar dokar dai majalisar dattawan sun ƙirƙiro ta ne kuma ta fara aiki ne a hukumance daga ranar da shugaba Buhari ya sanya hannu ta kuma zama doka wato ranar 31 na watan Mayun shekarar 2015 kenan.

Ba shakka, kalmomin dokar sun nuna tamkar da gangan aka tsara su da nufin hana Jonathan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa. Na tabbata wannan shi ne fahimtar takwarana Femi Falana. Abinda nake so abokina Falana da sauran lauyoyi bakiɗaya su gane shi ne, kamar yadda taken nan na shari’a dake cewa ‘prospicit non respicit’ wanda yake nufin doka takan cigaba ne ba baya ba. Saboda haka, a taƙaice a tawa fahimtar idan a yanzu za a ta da batun rantsar da Jonathan da aka yi a 2010 da 2011 a ce sabuwar dokar da aka kafa daga baya ta yi aiki a kansa, tamkar dokar ta koma baya ne ba cigaba ba kamar yadda taken ta ‘prospicit non respicit’ din ya bayyana,” inji shi.

A ƙarshe dai a yayin da ƙwararrun lauyoyin biyu da sauran lauyoyin ƙasar nan da ma fannin shari’a bakiɗaya suke cigaba da tafka muhawara ta musamman a kan batun, ga dukkan alamu babu ɓangaren da zai iya yin nasara har sai an gwada muhawarar tasu a kotun dokoki.

Sai dai ra’ayin marubucin nan a kan batun shi ne, duk da komai ka iya faru amma da wuya tanadin dokar ta sashe na 137 dake da ikon hana Jonathan sake fitowa takarar ya yi tasiri, sai dai idan Jonathan ɗin ya qi fitowa takarar. Kasancewar a Nijeriya muke, inda galibi ciki har da fannin shari’ar ƙirƙira da yin ƙorafi a kan dokoki aka iya ba tare da aiwatar da su ba.