Mahmoud Yakubu: An mayar da kwarya gurbinta – Tinubu Vanguard

Wata kungiya mai fatan ganin Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a zaben 2023, ta yabawa shugaba Buhari akan sake nada Farfesa Mahmoud Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa.

Darakta janar na kungiyar Dakta Johnny Ben ne ya bada sanarwa a Abuja, inda ya bayyanawa manema labarai cewa, “lallai a wannan mataki na amince wa da sake nadin, to an mayar da kwarya gurbinta”

Ya kuma kara da kira ga shugaban hukumar zaben, da ya dauki kwararan matakan da zasu samar da zabe nagari a kasar nan.

“Ko shakka babu, sake nadin nasa an mayar da kwarya gurbinta”

“ya zama wajibi a yaba wa shugaba Buhari da yayi wannan dogon hange, a kuma yaba wa majalisar dattawa da basu bata lokaci wurin amincewa da wannan hange ba”

Jawabin ya kara da cewa “Ko shakka babu, Farfesa Yakubu yayi rawar gani a lokacin da ya rike hukumar zaben a karo na farko. Saboda samar da nagartattun hanyoyin zabe da yayi.

“Muna kira ga shugaban da ya kara jajircewa, wurin daukar matakan da za su shawo kan sauran kananan matsalolin da ke addabar tsarin zabe a Najeriya.

Mista Ben yayi kira ga gwamnati da ta  tabbatar da gyaran fuskar da ake yi wa dokokin zaben, saboda a samu zabe nagari a kasar nan, kafin na da zuwan zaben 2023.

“Ya kara da cewa, samar da wannan gyaran fuska ga dokar ne, zai bai wa hukumar zaben damar yin ingantaccen zabe a shekaru biyu masu zuwa”.

In dai ba a manta ba, kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya hakaito cewa, shugaba Buhari ya gabatar da sunan shugaban na hukumar zaben ga majalisar dattawa, domin ya maimaita a karo na biyu. Kuma mako guda bayan haka, majalisar ta amince da nadin nasa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*