Mai shirin zama minista ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da tantance shi

Mai shirin zama Minista daga Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, ya yanke jiki ya faɗi a gaban ‘yan Majalisar Dattawa yayin da ake tsaka da tantance shi a ranar Laraba.

Da fari Balarabe ya yi jawabi na mintoci da dama kafin daga bisani ya yanke jiki ya zube a ƙasa.

An ga ‘yan majalisar sun yi ca a kan Balarabe bayan da ya zube a ƙasa domin ba shi agajin gaggawa.

Hakan ya faru ne bayan ya kammala jawabi yake kuma shirin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar.

Daga bisani, ‘yan majalisar sun je taƙaiccen hutu kafin farfaɗowar Balarabe.