Mai yiwuwa tsadar kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru da kashi 25 a ƙarshen 2023 – Bankin Duniya

Daga BASHIR ISAH

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa bayan cire tallafin mai da aka yi a Nijeriya, mai yiwuwa hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 ya zuwa ƙarshen 2023.

A cikin rahoton da ya haɗa game da ci gaban da Nijeriya ta samu na watan Yuni 2023, Bankin ya ce galibi hauhawar farashin zai shafi kayan abinci ne sakamon tsadar kuɗin mota da ake fuskanta tun bayan cire tallafin mai.

Bankin ya ce yanzu hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 22.41 wanda hakan ya jefa Nijeriya cikin jerin ƙasashen da suka fi fama da tsadar kayayyaki a faɗin duniya.

A jawabin da ya gabatar wa ‘yan ƙasa jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023, aka ji Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ‘yan Nijeriya cewar an cire tallafin mai.

Tare da cewa, zai karkatar da kuɗaɗen tallafin wajen ƙarfafa muhimman sassan tattalin arzikin ƙasar.

Tun bayan sanar da cire tallafin man ne farashin fetur ya cilla sama daga N189 zuwa sama da N500 kan lita guda.

Sai dai Bankin na duniya ya ce tsadar mai da Nijeriya ke gani a yanzu na wucin-gadi ne, yana mai cewa raɗaɗin cire tallafin zai sassauta a gaɓan farko na shekarar 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *