Fitaccen ɗan jarida a fannin ɗaukar hoto a Nijeriya, Sani Maikatanga, ya lashe gasar ɗaukar hoto ta ƙasa da ƙasa ta Wiki Loves Africa 2023.
Mutum 13,413 daga ƙasashen Afirka 51 ne suka shiga gasar.
Maikatanga ya yi wa takwarorinsa zarra a gasar ne ta dalilin wani hoto da ya ɗauka mai alaƙa da sauyin yanayi a ƙauyen Auyo, Jihar Jigawa.
Taken gasar na bana ya maida hankali ne kan sauyin yanayi.
Bayanan Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, (WHO), sun nuna sauyin yanayi matsala ce da kan shafi iskar da ake amfani da ita da ruwan sha da abinci da dai sauransu.
Ɗaya daga cikin alƙalan gasar, Juror Michale Maggas ya ce, “Hoton ya nuna haƙikanin al’amari a ƙauyukan da ambaliya ta shafa, yanayin launi da kuma kaifin sun sanya hoton maza mai ɗaukar hankali. “
A nasa ɓangaren, gwarzon gasar ta bana, Sani Maikatanga, ya yaba wa Wikki Loves Africa bisa yarda da aikinsa.
Ya ƙara da cewa, “Wannan karramawa ce ta haƙiƙa samun wannan sanayyar daga gare ku. Kalmomi kaɗai ba za su isa wajen bayyana yadda na ji dangane da da wannan karamcin ba.”
Dala 2000 ce tukwicin da aka ware wa wanda ya zo na ɗaya a gasar ɗaukar hoto ta Wikki Loves Africa ta 2023.