Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya musanta zargin da ake na cewa, majalisa ta 10 na yunƙurin sahale siyowa Shugaban Ƙasa da Mataimakin sa sabon jirgi.
Akpabio, a yayin zantawarsa da yan jarida a Maiduguri yace wannan zargin Ƙaryane kawai. A cewar wata sanarwa daga mai taimaka ma Akpabio ɗin na shafukan sada zumunta Jackson Udom, yace Kakakin Majalisar yaje Maiduguri ne domin yin ta’aziyya ga Sanata Mongunu sabida rashin mahaifinsa.
Akpabio yayi murna ƙwarai ganin yadda zaman lafiya ya dawo garin Maiduguri. Yace wannan kaɗan daga cikin irin jajircewa ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne.