Daga USMAN KAROFI
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da gabatar da gyare-gyare 44 a kundin tsarin mulkin ƙasar domin karantawa karo na biyu. Daga cikin muhimman gyare-gyaren da aka gabatar akwai yunƙurin cire kariyar ga mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu, wanda zai bar shugaban ƙasa shi kaɗai da kariya daga gurfanarwa a gaban kotu yayin da yake kan mulki.
Wannan matakin, wanda Hon. Solomon Bob ya ɗauki nauyinsa, an ce an yi shi ne domin hana cin hanci da rashawa, kawar da cin zarafi da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a cikin gwamnati.
A ɓangaren rarraba iko, wasu daga cikin ƙudurorin sun haɗa da sauya tafiyar da albarkatun ƙasa daga jerin ikon tarayya zuwa jerin ikon jihohi. Haka nan, an gabatar da ƙuduri kan sake fasalin titunan ƙasa, tare da ba da damar jihohi su kula da wasu manyan hanyoyi.
A fannin ‘yan ƙasa, majalisa ta amince da ƙudurori da suka haɗa da bai wa maza da suka auri ‘yan Najeriya damar zama ‘yan ƙasa, da kuma bai wa wanda suka zauna a jiha fiye da shekaru goma damar samun matsayin dan asalin jihar.
Haka zalika, an gabatar da kudurin kafa sabbin jihohi shida.