Majalisa ta amince da ƙudurin dokar da za ta bai wa gwamnati damar bai wa ɗalibai bashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince da ƙudurin dokar da za ta bai wa gwamnati damar bai wa ɗalibai bashi don su yi karatun gaba da sakandare.

Bashin yin karatun wani tsari ne da gwamnatin Nijeriya ke son ɓullowa da shi na bai wa ɗalibai bashi domin su cigaba da karatunsu na gaba da sakandare, kazalika bashin ana bayar da shi ne ga ɗalibin da yake karatu a Nijeriya kama tun daga matakin difiloma har zuwa digiri.

A Shekarar 2019 Femi Gbajabiamila ya gabatar da ƙudirin dokar da yake so a riƙa bai wa ɗalibai bashi domin su samu su yi karatun gaba da sakandare, wanda hakan yake nuna cewa gwamnati za ta daina ɗaukar nauyin ilimin gaba da sakandare kenan baki ɗaya, zai zama duk wanda zai yi karatun to sai ya riƙa biyan kuɗin makaranta, kuma ana hasashen kuɗin zai iya farawa daga 500,000 zuwa sama, ya danganta da abinda ɗalibi ke karanta.

Gwamnati za ta ƙirƙiri banki mai suna “Nigeria Education Bank” Wannan bankin shine aka ɗora wa alhakin bai wa ɗalibai bashin.

A cikin tsarin, an yi nuni da cewa duk ɗalibin da zai karɓi wannan bashin za a buɗe masa asusun ajiya da wannan bankin a ƙarƙashin Student Funds.

Haka kuma dokar ta cigaba da cewa duk ɗalibin da yake so ya karɓi bashin zai rubuta takarda ne zuwa ga shugaban bankin, ta hannun Students Affairs Division.

Kana ia kuma makarantar za ta tattara sunayen ku gaba ɗaya ta rubuta wasiƙa ta tura wa shugaban bankin da dai sauran abubuwan da za su taimaka wa ɗalibai.