Majalisa ta amince wa gwamnati kinkimo bashin bilyan $1.5 da milyan €995

Daga FATUHU MUSTAPHA

Bayanan da Manhaja ta samu ba da jimawa ba sun nuna Majalisar Dattawa ta amince wa Gwamnatin Tarayya da jihohi su kinkimo bashin Dala bilyan $1.5 da Yiro milyan €995 daga ƙetare.

Majalisar ta yi na’am da batun ciyo bashin ne bayan da ta yi nazarin rahoton da kwamitinta kan sha’anin rance ya gabatar mata.

Shugaban Kwamitin, Clifford Ordia, ya sanar da majalisar kwamitinsa ya gamsu da batun neman rancen kuma yana bada shawarar ita ma ta amince da batun.

Bashin Yiro milyan €995 da gwamnatin ta nema za ta yi amfani da kuɗaɗen ne wajen bunƙasa fannin noman zamani, yayin da za a sarrafa Dala biliyan $1.5 wajen kula da manyan ayyuka a ɗaukacin ƙananan hukumomi 774 da ake da su a faɗin ƙasa a tsakanin jihohi 36 har da birnin tarayya, Abuja, bayan lafawar guguwar annobar korona.

Ɓangarorin da za su taka rawa wajen karɓo bashin sun haɗa da Asusun Lamuni na Ƙasa da Ƙasa (IMF), da Bankin Duniya (World Bank) da Bankin Bunƙasa Afirka (AFDB) da kuma Bankin Hada-hadar Kasuwanci na Brazil.