Majalisa ta buƙaci Buhari ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaro

Daga WAKILIN MU

Majalisar dattijan Najeriya ta buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaron da suka addabi sassan Nijeriya.

Majalisar ta buƙaci haka ne bayan da ‘yan bindiga suka sace ɗalibai sama da 20 a Kwalejin Kimiyya ta Kagara, Jihar Nejs’a, a Larabar da ta gabata.

Sanata Sani Musa da ke wakiltar gabashin Jihar Neja, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin neman shelar dokar ta-ɓacin, ya ce ‘yan bindigar da suka sace ɗaliban na sanye ne da kayan sojoji.

Haka nan, Majalisar ta bumaci hukumomin tsaron Nijeriya da su kafa rundunar haɗin gwiwa sojoji da za a ɗora wa alhakin tarwatsa dukkanin sansanonin ɓarayi ko ‘yan bindigar da ke sassan ƙasa.

Sauran sanatocin da suka tofa albarkacin baki kan wannan batu, baki ɗaya sun tir da faruwar hakan. Tare da jaddada buƙatar gwamnati ta ƙara matse ƙaimi wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.