Majalisa ta dakatar da Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU

Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Jin Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Binciken Manhaja ya gano cewa an dakatar da Magaji ne saboda ƙin karɓar wani akawun da Akanta Janar na jihar ya tura hukumar.

‘Yan majalisun sun ce sun samu takardar ƙorafi daga ofishin Akanta Janar na Jihar daga Ma’aikatar Kuɗi ta Jihar bisa ƙin yarda da Magaji ya yi ya karɓi jami’in da aka tura hukumarsa a matsayin Babban Jami’in Kuɗi na hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *