Majalisa ta fara tantance sabbin ministoci guda bakwai da aka naɗa

Majalisar dattijai ta fara aikin tantance ministoci bakwai da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ranar Laraba da ta wuce.

An gudanar da wannan tantancewar ne a majalisar dattawa ranar Laraba, bayan da aka ɗage aikin a ranar Talata. Majalisar ta fara da Nentawe Yilwatda, wanda aka naɗa ya maye gurbin Betta Edu a matsayin ministan al’amuran jin ƙai da rage talauci.

Sauran ministocin sun haɗa da Bianca Odumegu-Ojukwu wadda aka naɗa ta zama ƙaramar ministan harkokin wajen Ƙasar, Maigari Dingyadi wanda aka naɗa ya zama ministan ƙwadago da kuma Jumoke Oduwole wadda aka naɗa ta zama ministan masana’antu.

Haka kuma akwai Idi Maiha a matsayin ministan ma’aikatar Kiwon dabbobi da aka ƙirƙiro sai Yusuf Ata a matsayin ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birni, tare da Suwaiba Ahmad a matsayin ƙaramar ministan ta Ilimi.

A ranar Laraba da ta wuce, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kori ministoci biyar, ya sauya wa ministoci 10 zuwa sabbin ma’aikatu, kuma ya naɗa sabbin ministoci bakwai don amincewar majalisar dattawa.