Majalisa ta gayyaci tsohon shugaban FMBN kan badaƙalar kwangilar bilyan N3

Daga AISHA ASAS

Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta mai bin diddigin ayyukan gwamnati (SPAC), ta kirayi tsohon shugaban Bankin Bada Bashi (FMBN), Malam Gimba Yau Kumo, da ya bayyana a gabanta kan badaƙalar kwangilar Naira bilyan N3 da aka bayar.

Kamar yadda rahoton da aka miƙa wa Ofishin Babban Jami’in Bincike na Ƙasa ya nuna, an bayar da kwangilar ne rukuni-rukuni har huɗu wanda hakan ya yi sanadiyar biyan kuɗi wuce abin da ya kamata a biya da Naira milyan N118,717,892.

Bayanan Odita Janar wanda Shugaban Kwamitin Majalisar, Sanata Mathew Urhoghide (PDP Edo ta Kudu), ya bayyana wa manema labarai a Juma’ar da ta gabata, sun nuna cewa, “An miƙa aikin kwangilar ne ga wani ɗan kwangila gutsu-gutsu har kashi huɗu a kan kuɗi N3,045,391,531.97.

“An lura da cewa kashi na biyu da na uku da na huɗu na kwangilar ya wuci bada izinin bankin.

“Haka ma an lura cewa an biya kuɗaɗen kwangilar fiye da abin da ya kamata a biya kamar yadda takardu suka nuna inda aka samu ƙarin N118,717,892.72, wato an samu ƙarin kashi 5.

“Sannan ziyarar gani da ido da aka kai wajen ayyukan, an gano an biya kuɗi milyan N80,000,000.00 domin samar da wata na’urar aiki, amma an tarar da na’urar ba ta aiki yadda yadda ake buƙata.

“An biya milyan N644,040,000.00 domin kula da sha’anin aiki yayin kashi na uku da na huɗu na kwangilar, amma babu wata ƙwaƙƙwarar shaida kan cewa an aiwatar da abubuwan da aka buƙata.”

Da yake bayani a gaban Kwamitin, shugaban FMBN, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya ce tun a 2011 aka bada kwangilar.

Yana mai cewa,”Jagorancin bankin da ya gabata ne ya bada aikin a 2011 a kan inganta tsarin bankin da zummar ƙirƙiro wata manhaja da za ta ƙunshi harkokin bankin baki ɗaya.”

Ya ƙara da cewa bayan da nasu jagorancin ya bincika tare da fahimtar abin da ke faruwa, ba tare da ɓata lokaci suka nuna rashin gamsuwarsu game da aikin ɗan kwangilar.

A ƙarshe, bayan nuna rashin gamsuwarsa game da ayyukan kwangilar, Shugaban Kwamitin ya umarci akawun Majalisar da ya rubuta wa shugaban bankin na dauri kan ya gabatar da kansa ga kwamitin a cikin wannan mako don yin bayani mai gamsarwa game da badaƙalar kwangilar.

Tare da buƙatar shugaban bankin mai ci ya taimaka wajen janyo masa tsohon shugaban bankin ba tare da wata gazawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *