Majalisa ta tabbatar da naɗin sabbin jakadu duk da ƙorafin da aka yi a kan su

Daga WAKILIN MU

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsoffin Shugabannin Tsaron Nijeriya a matsayin jakadu. Wanna ya faru ne a Talatar da ta gabata.

Idan ba a manta ba, a Janairun da ya gabata Shugaba Buhari ya zaɓi General Abayomi G. Olonisakin da Lt. General Tukur Y. Buratai da Vice Admiral Ibok-Ete E. Ibas da kuma Air Marshal Sadique B. Abubakar don zama jakadun Nijeriya bayan murabus da suka yi daga aiki ba da jimawa ba.

Amincewa da naɗin ya zo ne bayan gamsuwa da majalisar ta yi da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje ƙarƙashin jagorancin Adamu Muhammad Bulkachuwa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya ce, “Waɗanda muka tabbatar da naɗin nasu, mutane ne da suka yi wa ƙasa aiki gwargwadon iko.

“Roƙonmu gare su shi ne su yi amfani da saninsu a matsayinsu na sojoji don amfanin ƙasa.”

Tun farko sai da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Enyinnaya Abaribe, ya ja hankalin majalisar kan ƙorafin da majalisar ta yi game da zaɓen tsoffin sojojin, sai dai hakan bai yi wani tasiri ba.

Lawan ya ce, matsayar da majalisar ta cim ma na cire waɗanda lamarin ya shafa, batu ne wanda ba shi da alaƙa da buƙatar Shugaba Buhari na neman amincewar majalisa kan naɗa tsoffin jami’an a matsayin jakadu.

Ya ci gaba da cewa duba da irin sanin da jakadun ke da shi a fagen daga, ya kamata su iya assasa kyakkyawar mu’amala da ƙasashen da za a tura su don amfanin ƙasashen da Nijeriya.

Don haka ya ce, “Ba za a yi fatali da zaɓen su da aka yi ba tun da a wancan lokaci cewa muka yi a canja su.”