Majalisa ta tuhumi JAMB kan kashe biliyan N2 kan abinci da maganin ƙwari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dokokin Tarayyyar Nijeriya sun tuhumi Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) kan kashe kuɗin da suka wuce ƙa’ida kan abinci da lemu da ruwa da maganin sauro da sauransu a 2024.

Kwamitin ya yi barazanar cire hukumar daga jerin ma’aikatun da za su shiga cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na 2025.

Hakan na zuwa ne bayan da shugaban hukumar, Farfesa Ishaƙ Olayede ya gabatar da kasafin kuɗin hukumar na 2025 a gaban kwamitin na haɗin guiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

Olayede ya ce, JAMB ta samar da kuɗin shiga biliyan huɗu, yayin da gwamantin tarayya ta ba ta biliiyan shida.

Sai dai sanatan jihar Edo ta tsakiya, Adams Oshiomhole ya tuhumi JAMB kan kashe kuɗi masu yawa, inda ya buƙaci shugaban hukumar ya yi cikakken bayani kan yadda suka kashe naira miliyan 850 kan tsaro da share-share da kuma feshin kashe ƙwari a shekarar da ta gabata.

“Kun kashe sama da biliyan ɗaya kan abinci da lemuka.Shin gwamnatin tarayya ke ciyar da ku kyauta? Abinda hakan ke nufi shi ne, kuna kashe kuɗin da kuke ƙarɓa daga ɗalibai marasa galihu waɗanda da yawansu marayu ne. Kun kuma kashe naira miliyan 850 kan tsaro da share-share da feshin ƙwari a 2024. Wadanne irin ƙwari ne kuma kashe? Shin sauro ne ya ɗauki dukkan kuɗaɗen?”

Oshiomhole ya kuma ƙalubalanci hukumar kan kashe miliyan 600 wajen tafiye-tafiyen cikin gida.

Tun da farko, shugaban kwamitin, Sanata Musa ya bayyana damuwarsa kan ƙarancin kuɗaɗen shiga da ma’aikatu, ma’aikatu da hukumomi da wasu kamfanoni mallakar gwamnati suka samu a shekarar 2024, zuwa asusun tarayya.

Hukumomi a wajen taron sun haɗa da Hukumar Kwastam ta Nijeriya, NCS, Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya, FRSC, da Hukumar Shirya Jarrabawa da Matriculation ta JAMB.

Sanata Musa ya bayyana cewa majalisar dattawan ta damu matuƙa game da ƙaruwar banbance-banbance tsakanin ɗimbin kuɗaɗen shiga da ake samu ga hukumomi da kuma ƙarancin kuɗaɗen da suke turawa a asusun tarayya.

Ya ce, “Wannan yanayin yana lalata ikon gwamnati na samar da muhimman ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a, yana mai yin tambaya kan batutuwan da suka shafi gazawa, rashin gudanar da aiki da kuma yuwuwar taɓarɓarewar kuɗaɗen shiga.”

A cewarsa, aikin kwamitin shi ne tabbatar da gaskiya, riƙon amana da inganci a harkokin kuɗi na hukumomin.

Ya kuma ce kwamitin zai ci gaba da bin diddigin hasashen kuɗaɗen shiga na hukumomi, yadda ake gudanar da aiki da kuma bin ƙa’idojin aikawa da kuɗaɗe na doka.

Musa, wanda ya bayyana cewa taron shi ne don gano shakku bisa tsari tare da ba da shawarar sakamako mai dacewa don sauya yanayin da ke damun al’amura, amma ya nemi haɗin kai da fahimtar duk masu ruwa da tsaki a zaman tattaunawa.

Ya ce ya zama wajibi a gabatar da sahihin bayanai, cikakkun bayanai da buɗaɗɗiyar bayanai domin amfanin ’yan Nijeriya.

“Bari mu tunkari waɗannan ayyuka tare da sadaukar da kai don gina ingantacciyar tsarin kasafin kuɗi na Nijeriya.

“Ina kira ga dukkanmu don Allah mu fito fili a duk wuraren da muka sani, koda kuwa ba a gabatar mana da su ba,” inji shi.