Majalisa ta yi tir da yadda jami’an kwastam ke buɗe wa jama’a wuta ba bisa ƙa’ida ba a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Majalisar Dattawa ta Nijeria ta yi Allah-wadai game da buɗe wutar da wasu jami’an hukumar kwastam suka yi a kan mutanen da ba su ji ba, basu gani ba a Jihar Katsina.

Majalisar ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta kuma buƙaci hukumar da ta gudanar da bincike kan lamarin.

Hakan na ƙunshe ne cikin wani ƙuduri da sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Sanata Abdul’Aziz Musa ‘Yar’adua, ya gabatar a zauren majalisar inda ya buƙaci majalisar ta gaggauta gudanar da bincike bisa yadda jami’an hukumar a jihar Katsina ke amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ƙudurin bai rasa nasaba da harbe-harben da jami’an hukumar suka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Idan za a iya tunawa, Manhaja ta kawo labarin yadda wasu jami’an hukumar ta Kwastam suka buɗe wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Alhaji Jabir Tsauri wuta a garin Gorar ‘Yammama cikin ƙaramar hukumar Malumfashi a hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Da fari an yi zargin ‘yan fashin daji ne suka buɗe wa motar Shugaban ma’aikatan wuta, kasancewar kwastam ɗin na sanye da farin kaya lamarin da ya tilasta masa tserewa shi da direbansa don tsira da ransu.

Tsauri ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa wasu mutane da suka rufe fuska sun yi yunƙurin halaka shi ba don Allah ya tseratar da shi ba.

Hotunan da ya wallafa sun nuna yadda harsasai suka huda tayoyin motarsa.

Ya ci gaba da cewa bayan da ƙura ta lafa waɗanda suka yi harbin sun bayyana masa cewar su jami’an hukumar kwastam ne.

A martanin da ya mayar dangane da faruwar lamarin Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya nuna damuwarsa dangane da yadda jami’an hukumar ke harbin al’umar jihar ba tare da sun aikata wani laifi ba, inda ya buƙaci hukumomin tsaro a jihar da su binciki musabbabin harin cikin gaggawa.

Cikin ƙudurin da ya gabatar a majalisa, Sanata ‘Yar’adua ya bayyana cewar ya yarda doka ta sahale wa jami’an hukumar amfani da bindigogi lokacin gudanar da aikinsu don yaƙi da masu fasa ƙwauri, sai dai ya nuna damuwarsa dangane da yadda jami’an kwastam a jihar ke amfani da makamai ba tare da bin doka ba.

Ya bayar da Misali a kan harbin da jami’an hukumar suka yi wa Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu a gwamnatin da ta gabata, da kuma na Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar a makon da ya wuce, gami da al’umar jihar da jami’an kwastam ɗin suka yi sanadiyyar jikkatawa a yayin da wasu suka rasa rayukansu a iyakar Nijeria da Nijar dake Jibiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *