Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dattijai ta shirya ƙwarya-ƙwaryar kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin yin zagon-ƙasa wa ɓangaren man fetur a Nijeriya.
Mataimakin shugaban Majalisar, Barau Jibrin ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar bayan da shugaban kwamitin, Opeyemi Bamidele ya ɗauki nauyin ƙudirin wanda ke neman Majalisar da ta Wakilai da su gudanar da binciken ɓangaren man.
Shugaban kwamitin ya ce Majalisar Wakilai ta gudanar muhawara akan batun wanda ita ma ta shirya kwamitin da zai yi bincike akan lamarin.
Ya kuma nemi su haɗa hannu tare da sanya wa kwamitin suna kwamitin haɗin-gwiwa na Majalisa da zai yi bincike kan zargin zagon-ƙasa a masana’antar ta man fetur.
Haka nan, ya nemi Majalisar Wakilan ta zaɓi adadin mambobin da za su yi aikin dai-dai da adadin da ta Dattijan ta samar.