Majalisar Dattawa ta sake bai wa CBN umarnin ƙara wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta sake umartar Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya gaggauta ƙara wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira ya zuwa 31 ga Yuli, 2023.

A ranar 15 ga Disamban da ya gabata CBN ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira na N200, N500 da kuma N1000, inda ya tsayar da 31 ga Janairu a matsayin lokacin da za a daina amfani da tsoffin takardun Naira da aka canza.

Idan dai za a iya tunawa, a Disamba, 2022 Majalisar Dattawa ta bai wa CBN umarnin tsawaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira, amma bankin ya yi biris da umarnin.

Wa’adin na CBN ya haifar da ruɗani a ƙasa yayin da lokaci ke daɗa ƙaratowa, lamarin da ya haifar da samun cunkoso a bankuna sakamakon neman canjin sabbin kuɗi da jama’a ke ribibin yi.

Yayin zamansu a ranar Talata, sanatoci sun tafka muhawara mai zafi kan ƙarancin sabbin takardun Naira.

Kazalika, sun yi gargaɗin muddin ba a tsawaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira ɗin ba, hakan zai haifar da ruɗani a sassan ƙasa.

Sun kuma nuna damuwarsu kan yadda CBN ya ƙeƙashe ƙasa, inda ya ce babu gudu ba ja da baya dangane da wa’adin 31 ga Janairu da ya tsayar don daina karɓar takardun Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *