Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin shugabannin hukumomin tsaro, waɗanda sabon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa.
Majalisar Dattawa Nijeriya ta tabbatar da sunayen mutanen a ranar Alhamis, 13 ga Yuli, 2023, bayan tantance su a wani zaman sirri da aka kwashe sama da awa ɗaya ana yi.
Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya ce yayin zaman sirrin, shugabannin hafsoshin sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma batutuwan da suka jivanci hakan.
Shugaban ƙasar a cikin wata wasiƙa da aka karanta a ranar Litinin a zauren majalisar ya buƙaci majalisar ta tabbatar da shugabannin tsaron.
Majalisar Dattijai, bayan dawo da zamanta a ranar Alhamis, ta fara tantance hafsan hafsoshin, inda kowannen su ya hau dandali domin yin magana kan yadda za su magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan idan har ta tabbata.
Hafsan hafsoshin da aka tabbatar sun haɗa da Manjo Janar C.G Musa (Babban Hafsan Tsaro), Maj. Gen. T. A Lagbaja (Babban Hafsan Sojojin Ƙasa), Rear Admiral E. A Ogalla (Babban Hafsan Sojin Ruwa), AVM H.B Abubakar (Babban Hafsan Sojan Sama), IGP Kayode Egbetokun (Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya), Maj. Gen. EPA Undiandeye (Babban Hafsan Tsaro).
Idan za a iya tunawa, a ranar 19 ga watan Yuni, 2023, makwanni uku kenan da rantsar da shi, Tinubu ya tsige shugabannin ayyuka a Nijeriya tare da naɗa sabbin waɗanda ya umurce su da su ci gaba da aiki nan take.
Waɗanda abin ya shafa a girgizar da ba a tava ganin irinta ba sun haɗa da Alkali Usman wanda aka tsige shi daga muƙamin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Lucky Irabor, wanda aka kora daga mukamin babban hafsan tsaron kasa; Faruk Yahaya, ya yi ritaya a matsayin babban hafsan soji; Awwal Gambo, wanda aka tsige a matsayin hafsan hafsoshin ruwa; da Isiaka Amao, mai ritaya a matsayin babban hafsan hafsoshin sojin sama.
Daga nan ne shugaban ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro tare da naxa tsohon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC Nuhu Ribadu a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro (NSA).
Ribadu ya maye gurbin Babagana Monguno a matsayin NSA na Ƙasa.
Tinubu ya kuma naɗa Adeniyi Adewale a matsayin muqaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom.
Tuni dai dukkan sabbin naɗe-naɗen da aka naɗa suka koma bakin aiki kafin majalisar dokokin qasar ta tabbatar da su.