Majalisar Dattawa ta tsawaita bincike kan zargin NDDC da yin mu’amalar kuɗaɗe ba tare da izini ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattijai ta bada ƙarin lokaci ga kwamitin wucin-gadi da ta kafa domin binciken wasu maƙudan kuɗaɗe da ake zargin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta yi mu’amalarsu ba tare da izini ba.

Kwamitin wanda Yusuf Yusuf (APC, Taraba ta Tsakiya) ya jagoranta, an kafa shi ne a zaman majalisar a ranar Talatar da ta gabata, domin gudanar da bincike kan ma’amalolin da hukumar ta NDDC ta yi a kasafin kuɗinta na 2021 da 2022 ba tare da amincewar majalisar dattawa ba.

Majalisar dattijai ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa cikin mako guda.

Sai dai a zaman da aka koma, majalisar a ranar Talata, shugaban kwamitin ya ce babu ɗaya daga cikin waɗanda ke da alaƙa da zargin da aka tattauna da su.

Yusuf ya roƙi ‘yan majalisar na tsawaita wa’adin mako guda domin kwamitin ya gudanar da binciken da ya dace kan zargin.

“Muna neman yardar Majalisar Dattawa ta ba mu mako guda saboda ba mu yi hira da kowa ba a wannan lokacin,” inji shi.

Don haka Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ƙara wa’adin mako guda, sannan ya buƙaci ‘yan kwamitin da su tabbatar sun gudanar da bincike mai inganci kan zargin.