Majalisar Dattawa za ta gana da hafsoshin tsaro kan sha’anin tsaron ƙasa

Daga AISHA ASAS

A ranar Alhamis ake sa ran Majalisar Dattawa ta karɓi baƙuncin manyan hafsoshin tsaron ƙasa da sauran hukumomin tsaro inda za a tattauna kan batun da ya shafi matsalolin tsaron ƙasa.

Manhaja ta fahimci cewa buƙatar gayyatar jami’an ta taso ne duba da yadda sha’anin tsaron ƙasa ke ƙara daburcewa.

Tun farko, Majalisar ta so ganawa da Shugaban Rundunar Sojoji da Babban Sufeton ‘Yan Sanda da kuma Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), a Talatar da ta gabata amma sai hakan bai yiwu ba sakamakon taron majalisar tsaro ta ƙasa ta gudanar.

A bisa wannan dalili ne Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan, ya roƙi takwarorinsa kan a ɗage batun zuwan hafasoshin tsaron ya zuwa Alhamis, 6 ga Mayu, 2021.

Ahmed Lawan, ya ce a makon da ya gabata majalisar ta yanke shawarar gayyatar jami’an da lamarin ya shafa domin jin ta bakinsu dangane da halin da fannin tsaron ƙasa ke ciki.

Lawan ya ce ganawar da za su yi da hafsosjin tsaron aba ce mai matuƙar muhimmanci, don haka ya buƙaci takwarorinsa da su ba da cikakken haɗin kansu idan lokacin ya zo.

Daga nan, shugaban majalisar ya bada tabbacin cewa sauraron bayanan shugabannin tsaron shi ne batun da majalisar za ta maida hankali a kansa a ranar Alhamis idan Allah ya kai mu.