Majalisar dokoki ta buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a garin Yashe da Daɗin Kowa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokoki a jihar Katsina ta amince da ƙudurin tunatarwar na gina magudanun ruwa a mazabar Yashe a karamar hukumar Kusada, tare da gina gada a ƙauyen Daɗin Kowa a ƙaramar hukumar.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada, Hon. Gali Garba ya gabatar da ƙudirin na tunatarwa ga ɓangaren zartarwa na gina magudanan ruwa a mazabar Yashe a ƙaramar hukumar Kusada.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa samar da wannan hanyoyin ruwa a garin zai taimaka wajen hana zaizayar ƙasa da garin yake fama dashi.

Ƙudirin na biyu, ƙudiri ne da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari, Hon. Mustapha Tukur Ruma ya gabatar inda ya nemi ɓangaren zartarwa da ta gina gada a ƙauyen Daɗin Kowa a ƙaramar hukumar Batsari.

Ɗan majalisar yace gadar tana da muhimmanci ga rayuwar al’ummar yankin domin a cewar sa za ta haɗa garuruwa da dama a yankin.

Hon. Mustapha Tukur Ruma yace”Gadar za ta taimaka wajen sauƙaƙa safarar kayan abinci da ake nomawa a garuruwan dake haɗe da Daɗin Kowa.

Haka kuma manoma zasu sami sauƙin kai amfanin gona su ba tare da wata matsala”Ruma ya ce.

Akan haka Hon Mustapha Ruma ya buƙaci zauren ya goya mashi baya domin Gwamnati ta aiwatar da ƙudirin.

Bayan tattaunawa akan ƙudirorin, mataimakin kakakin majalisar, Rt. Hon. Abduljalal Haruna Runka, ya umarci akawun majalisar ya mika koken a ɓangaren zartarwa domin ɗaukar mataki.