Majalisar Dokoki ta tsige Lamiɗon Adamawa a matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta amince da ƙudirin doka na kafa sabbin masarautu tare da naɗa sarakuna masu daraja ta ɗaya a jihar.

Sabuwar dokar masarautun, wadda ke jiran amincewar Gwamna Ahmadu Fintiri, ta samu amincewa ne kwana ƙalilan bayan gwamnan ya rattaɓa hannu kan wata doka, Dokar ƙirƙiro Gundumomi ta Jihar Adamawa 2024, wadda ta samar da sabbin gundumomi guda 83 a ranar 4 ga Disamba.

A wata wasiƙa da Mr. Fintiri ya aike wa ‘yan majalisar a ranar Litinin, ya buƙaci su amince da ƙudirin doka da zai bayar da damar naɗa sarakuna da cire su daga muƙamansu a jihar Adamawa.

Kudirin ya bai wa gwamnan ikon kafa ƙarin masarautu tare da naɗa ko tsige shugabannin gargajiya.

Kudirin dokar ya tsallake karatun farko da na biyu a Majalisar Dokokin Jihar a ranar Litinin.

Dokar ta rage tasirin Lamiɗon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo, ta hanyar taƙaita yawan ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashinsa daga takwas zuwa uku.