Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Godswill Akpabio, ya bayyana bayyana cewa, Majalisar Dokokin Nijeriya ta gamsu da ayyuka da matakan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka.
Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaban ƙasar.
Ya ce, majalisar za ta haɗa hannu da vangaren zartarwa na gwamnati domin inganta rayuwar ’yan Nijeriya.
“Shugaban ƙasa ya riga ya fara ayyuka, kawai yana buƙatar goyon bayanmu ne don cigaban ayyukan a ƙasa. Don haka, majalisar da za ta dawo aiki, za mu kuma ba da shawarar mu ga abin da muka gani ya zuwa yanzu. Ya ɗauki matakan da suka dace.
“Kasuwar hannayen jari na ƙaruwa kuma mutane da yawa sun yi matuƙar farin ciki da matakan da ya ɗauka ya zuwa yanzu. Akwai sabon fata ba kawai ta fuskar tattalin arziki ba amma ta fuskar zaman lafiyar ƙasar kuma hakan zai shafi dukkan ɓangarori na rayuwa ciki har da tsaro.
“Don haka ina yaba masa kuma muna maraba da wannan ci gaban ya zuwa yanzu. A matsayinmu na Majalisar Dattawan Tarayyar Nijeriya mu mara masa baya da dokokin da suka dace sannan kuma mu fito da mafi yawan al’amuran da ke faruwa a mazavunmu daban-daban ta hanyar gabatar da ƙudiri da lura domin gwamnati ta ƙara ɗaukar matakai tun da dai mun fi kusa da tushen,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko me ’yan Nijeriya za su yi tsammani daga ’yan majalisar, Akpabio ya ce, majalisar za ta tabbatar da muhawara mai ƙarfi da kuma yanke shawarar da za ta inganta rayuwar ’yan Nijeriya.
“Ya kamata su yi tsammanin zafafan muhawarar majalisa. Su yi tsammanin za mu mai da hankali kan Nijeriya kuma su sa ran mu taimaka wa shugaban ƙasa ya yanke shawarar da za ta taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma yanke shawarar da za ta tabbatar da qarfafawa ‘yan Nijeriya gaba ɗaya.
Ya ce, babban abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai shi ne batun tsaro da jin daɗin rayuwar jama’a, inda ya ce, ’yan majalisar tare da sauran ɓangarorin gwamnati sun shirya yin hakan.