Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da ƙudirin dokar ƙirƙiro da sabbin gundumomi guda shida a masarautar Katsina da Daura.
Amincewar majalisar akan ƙudirin dokar kirkiro da sabbin gundumomin ya biyo bayan doguwar muhawara da majalisar ta yi.
Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Raɗɗa ya turama majalisar buƙatar ƙarin gundumomin wanda kakakin majalisar dokokin Rt Hon Nasiru Yahaya ya gabatar a zauren majalisar.
Gundumomin da gwamnan ya buƙaci majalisar tayi dokar ƙirƙiro da su, sun haɗa da Raɗɗa daga gundumar hakimin Charanci da ke cikin ƙaramar hukumar Charanci, Dankama daga gundumar hakimin Kaita da ke cikin ƙaramar hukumar Kaita.
Sai Dabai daga gundumar hakimin Ɗanja dake cikin ƙaramar hukumar Danja, Muduru daga gundumar hakimin Mani da ke cikin ƙaramar hukumar Mani. Dukkan su daga yankin masarautar Katsina.
A yankin masarautar Daura kuwa za a ƙirƙiro gundumar Dankum daga gundumar hakimin Yanduna da ke cikin ƙaramar hukumar Ɓaure, yayin Kawarin kuɗi da ke cikin ƙaramar hukumar Zango za a fidda ta daga gundumar hakimin Yardaje.
Duk a zaman majalisar na ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Mani Hon. Shu’aibu Zayyana Bujawa ya gabatar da ƙudirin mayar da makarantar jeka ka dawo ta garin Mani da ta koma makarantar kwana.
Bayan tattaunawa da ɗaukacin ‘yan majalisar su ka yi, daga ƙarshe majalisar ta amince da ƙudirin, inda Kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya turama ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.