Majalisar Dokokin jihar Yobe ta zaɓi Hon. Mashio a matsayin Kakakinta

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Hon. Chiroma Buba Mashio daga mazaɓar Jajere, ya zama sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, zubi na 8.

Hakan ya biyo bayan zaman da majalisar ta ƙaddamar a ranar Litinin a zauren majalisar dake Damaturu.

Sa’ilin da aka fara gabatar da ƙudirin zaɓen sabon Kakakin Majalisar, wanda Hon. Adamu Dala Dogo mai wakiltar mazaɓar Karasuwa ya gabatar inda ya samu goyon bayan Hon. Bukar Mustapha na mazab’ɓar Geidam ta tsakiya tare da samun amincewar dukkanin ‘yan majalisar dokokin su 24.

An haifi Hon. Buba Mashio ne a ranar 25 ga Mayu, 1968 a garin Mashio na Ƙaramar Hukumar Fune dake Jihar Yobe.

Ya fara karatun sa a firamaren Mashio sannan ya wuce Sakandaren Gwamnati dake Damagum, kuma ya fara aiki a Ƙaramar Hukumar Fune inda ya yi murabus ya tsaya takarar kansila mai wakiltar Gundumar Mashio, inda daga bisani ya zama Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar.

A ƙoƙarinsa na ci gaba da karatunsa, sabon Kakakin ya garzaya inda ya yi Diploma a Ramat Polytechnic Maiduguri, da Digirinsa na farko a Jami’ar Maiduguri a fannin kimiyyar siyasa.

Mashio ya tsaya takarar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar mazaɓar Jajere a 1999, ya yi aiki a kwamitoci da muƙamai daban-daban a zauren majalisar.

Sauran manyan ƙusoshin majalisar sun haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Yau Usman Dachia, Shugaban Majalisar, Hon. Nasiru Hassan Yusuf, Mataimakinsa, Hon. Hassan Muhd ​​Yusufari, Mai.Tsawatarwa a zauren majalisar, Hon. Muhammed Auwal Isa Bello, mataimakinsa, Hon. Ahmed Musa Dumbu.

A jawabinsa na godiya, sabon Kakakin majalisar, Chiroma Buba Mashio ya bayyana jin daɗinsa ga takwarorinsa bisa ga damar da suka ba shi ya jagoranci zauren majalisar na 8, tare da ɗaukacin al’ummar jihar baki ɗaya.

Mashio ya yi alƙawarin samar da ingantaccen shugabanci “ba tare da nuna son kai ba; tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya zai jagorance ni. Zan aiwatar da manufar buɗe ƙofa don maraba da shawarwari don inganta shugabanci nagari don samar da ingantacciyar doka.

Shugaban Majalisar ya bada tabbacin yin aiki cikin kwanciyar hankali da ɓangaren zartaswa da ɓangaren shari’a domin a samar da shugabanci nagari a jihar Yobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *