Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar dokokin jihar Legas a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da 22 daga cikin 39 da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya aika kwanan nan domin tantance su a matsayin kwamishinonin sa.
Kakakin majalisar Rt. Hon. Mudashiru Obasa, wanda ya jagoranci zaman na ranar, ya ce tabbatar da hakan ya biyo bayan tsaiko da tantance mutanen da kwamitin wucin gadi ƙarƙashin jagorancin babban mai shigar da ƙara na majalisar, Hon. Fatai Mojeed.
Ya yaba wa kwamatin kan yadda yake gudanar da ayyukansa, ya kuma buƙaci waɗanda aka zaɓa da su riƙa tunawa da cewa suna kan muƙaman ne domin yi wa al’ummar jihar hidima ba ɗaiɗaikun mutane ba.
Ya kuma yi alƙawarin cewa majalisar za ta ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinta domin amfanin jihar.
An tabbatar da hakan ne ta hanyar kaɗa ƙuri’a yayin da Dokta Obasa ya ambaci sunan kowane ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa.
Sai dai ‘yan majalisar sun qi amincewa da 17 daga cikin waɗanda aka naɗa.
Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da: Hon. Layode Ibrahim; Mr. Mobolaji Ogunlende; Dr. Dolapo Fasawe; Hon. Bola Olumegbon; Malam Idris Aregbe; Madam Abisola Ruth Olusanya; Mr. Moruf Akinderu Fatai; Mr. Kayode Bolaji-Roberts.
Sauran sun haɗa da: Engr. Abiola Olowu; Mrs. Toke Benson-Awoyinka; Dr. Oreoluwa Finnih-Awokoya; Malam Yakub Adedayo Alebiosu; Mr. Lawal Pedro SAN; Malam Tunbosun Alake; Mr. Gbenga Oyerinde; Dr. Adekunle Olayinka; Dr. Jide Babatunde; Mr. Afolabi Aintayo.
Haka kuma akwai: Malam Tokunbo Wahab; Mr. Olakunle Rotimi-Akodu; Malam Jamiu Alli-Balogun da Malam Abdulkabir Ogungbo.
Waɗanda majalisar ba ta tabbatar ba sun haɗa da: Madam Folashade Adefisaya; Farfesa Akin Abayomi; Mista Yomi Oluyomi; Madam Folashade Ambrose; Madam Barakat Bakare; Mr. Gbenga Omotosho; Engr. Olalere Odusote; Dr. Rotimi Fashola; Madam Bolaji Cecilia Dada; Mista Sam Egube; Mr. Olalekan Fatodu; Madam Solape Hammond.
Sauran su ne: Mr. Mosopefolu George; Engr. Aramide Adeyoye; Mr. Seun Osiyemi; Mr Rotimi Ogunwuyi da kuma Dr. Olumide Oluyinka.
Kafin a fara atisayen, Hon Mojeed Fatai ya yi wa majalisar bayanin sakamakon aikin tantancewar.