Majalisar Ministoci ta cire hannunta kan batun mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar ministoci (FEC), ta ce ta janye daga tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashin ma’aikata, domin bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu damar cigaba da neman shawarwari da masu-ruwa-da-tsaki kan batun.

Ministan harkokin yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Mohammed ya faɗi hakan a yayin hira da wakilan fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a ranar Talata.

Idris ya ce, shugaba Tinubu ya yi nazari kan rahoton kwamitoci uku na tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashin, sannan kuma zai yi shawara da waɗanda lamarin ya shafa kafin miƙa sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata ga majalisar ƙasa.

Tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi, abu ne da ake yi tsawon lokaci a Najeriya, inda a shekarar 2019, naira dubu 30 ne mafi ƙarancin albashi wanda wa’adinsa ya ƙare a watan Afrilun shekararnan yayinda akwai buƙatar a sauya shi, saboda tsarin ya dace da yanayin tattalin arziƙin ƙasa ga ma’aikatan.

Tun a watan Janairun shekararnan ne shugaba Tinubu ya naɗa kwamitoci da za su tattauna da wakilan ƙungiyar ƙwadago da na haɗaɗɗun kamfanoni kan lamarin.

Bayan tsawon tattaunawa a tsakaninsu, ba a samu yarjejeniya ba, domin gwamnati ta ce za ta ke biyan dubu 62 yayin da ƙungiyoyin ƙwadago suka ce sai dai ta ke biyan dubu 250.